✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mulkin Jari-Hujja ne matsalar Najeriya – Dokta Fagge

A kwanakin baya ne kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta gudanar da taro a Kalaba a karkashin jagorancin shugabanta Dokta Nasiru Isah Fagge. Bayan…

A kwanakin baya ne kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta gudanar da taro a Kalaba a karkashin jagorancin shugabanta Dokta Nasiru Isah Fagge. Bayan kammala taron shugaban ya yi wa Aminiya karin haske game da batutuwan da suka tattauna da suka hada da matsalar tabarbarewar tsaro da bullar cutar Ebola da kuma uwa-uba matsalar shugabanci da ya dora alhakin lalacewarsa kan mulkin Jari-Hujja a Najeriya:

Aminiya: Me kuka tattauna a wurin taronku na shugabannin kungiyar ASUU?
Dokta Nasiru Fagge: Mun tattauna ne a kan abubuwan da suke faruwa a kasar nan musamman rashin tsaro da cututtukan da suke shigowa kasar nan suna daukar rayukan ’yan Najeriya. To shi ne muke ganin cewa matsalolin fa sun fi karfin yadda ake gani a zahiri, matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da irin mulkin da aka cusa wa ’yan Najeriya ba karfi da yaji. Wato wannan mullki na Jari-Hujja, mulki ne da shugaba ba ya sa damuwar talaka a ransa. Abin da ke ransa shi ne ta yaya zai yi ya tara dukiya wadda shi da iyalansa za su ji dadi, sauran jama’a kuma ohonsu! To abin da yake faruwa ke nan a kasar nan, shi ya sa muka ce ya kamata mu zo mu fadakar da jama’a yadda za mu hada kai a samu a yi wa bakin zaren tufka.
Mu a ganinmu na wadanda suke harkar bincike kan ilimi da aiwatar da shi da koya wa mutane, mun fahimci cewa mafitar da ta dace da Najeriya ita ce a samu salon mulki da zai mayar da hankali kan yadda za a kyautata wa talaka da marasa karfi. Mun lura cewa shi kansa kundin tsarin mulki na kasar nan ba a yi shi yadda zai kare hakkin talaka ba. Amma duk da raunin kundin tsarin mulkin idan ka lura su kansu masu aiwatar da mulkin ba sa bin tsarin mulkin ma yadda yake kuma sun yi rantsuwa cewa da wannan tsarin mulkin za su kare shi kuma sun aiwatar da shi.
Aminiya: Idan mun fahimce ka zargin ASUU shi ne matsalolin da kasar nan take fuskanta rashin kyakkyawan shugabanci ne?
Dokta Nasiru Fagge: Shi yanayin mulkin ma yana da matsala. Yanayin mulkin, yanayin mulkin Jari-Hujja ne shi kuma Jari–Hujja abin da ya sa a gaba shi ne kara wa mai karfi karfi da kara raunata mara karfi. Aminiya: Wani zai iya cewa kamar adawa ce kuke nuna wa gwamnati lura da yadda a watannin baya sai da kuka kai ruwa rana tsakaninku da ita kan wasu hakkokinku?
Dokta Nasiru Fagge: To ai ba maganar adawa a nan, abin da muke fada shi ne yaya za a yi a ce ana mulki, amma talakwan Najeriya ba su da kwanciyar hankali? Yau idan fa ka fita daga gidanka ba ka da tabbacin cewa za ka koma gida lami-lafiya. Ko dai a sace ka, ko a kashe ka, yanzu ma abin takaicin shi ne muna samun labarin cewa su kansu jami’an tsaro wadanda ake biyan su domin su tsare rayukan jama’a da dukiyarsu akan samu yanayin da cewa idan sun je za su yi aikinsu maimakon su kama masu laifi sai su buge da kama marasa laifi, to, ka ga wannan ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba.
Aminiya: Idan haka mene ne takamaiman abin da ASUU take bukata?
Dokta Nasiru Fagge: Abin da muke gani shi ne kamata ya yi duk wanda ya damu da Najeriya da mutanen Najeriya, ya zo a hada karfi-da- karfe ta yadda za a ceto kasar nan. Kuma muna ganin abin da ya kamata mu fara yi shi ne mu canja salon yadda ake mulkin kasar nan, yadda zai zamanto duk abin da gwamnati za ta yi abu ne da talakawa suke so kuma zai yi wa talakawa amfani. Alal misali a ’yan kwanakin nan an fito da wasu takardu ana nuna cewa wai tattalin arzikin kasar nan ya samu bunkasa, to amma kuma abin takaici shi ne idan ka koma ka ga talakawan Najeriya harkar rayuwarsu sai kara tabarbarewa take yi. Yaya za a yi a ce ana samun bunkasar tattalin arzikin kasa kuma a hannu daya talakawa ba sa gani a kasa?
Aminiya: Jawabin da ka gabatar kun bi ta barawo, amma ba ku bi ta mabi sawu ba, wato su talakawan da suke bari ana amfani da su da zarar an cimma buri a watsar da su, me za ka ce?
Dokta Nasiru Fagge : To shi wanda aka talauta aka sanya shi a cikin kangin talauci yana cikin matsala yana cikin bala,i me kake ganin zai iyayi? Abin da muke gani su talakawan Najeriyar nan wayar musu da kai ya kamata a yi, idan an wayar musu da kai za su fahimci cewa an sanya su ne fa a c ikin talaucin nan, tunda idan an yi amfani da dukiyar kasar nan yadda za a tabbatar da wadanda suke da ikon yin aiki sun samu aiki su fahimci ma yadda za su kirkiro ayyukan yi, mutane su samu aiki idan muka yi haka za mu yi maganin duk wani kangin talauci da yake damunmu a magance rashin tsaron nan da muke fama da shi.
Aminiya: Ina mafita da kuma shawarar ASUU?
Dokta Nasiru Fagge: Mafita kawai ’yan Najeriya su sake tunani mu canja salon mulkin da muke da shi a kasar nan, ya zamanto ba tsarin Jari-Hujja muke yi ba, ya kasance tsari ne wanda yake yana da asali da tsari irin na rayuwarmu ta ’yan Afirka, tunda rayuwarmu ta ’yan Afirka ba rayuwace ta zalunci ba, an san cewa tuntuni a Afirka duk dan Afirka yana kula da dan uwansa, yana taimakon dan uwansa, kuma idan ka ga dan uwanka zai shiga bala,i  za ka fito ka yi kokarinka ka ga ka taimaka masa ka hana shi shiga wannan bala’in. To abin da muke tunani shi ne idan aka wayar wa talakawa kai suka hada kai da ma’aikata da wadanda ba sa da aiki da wadanda ake cuta a kasar nan za a fitar da kasar nan daga kangin da take ciki, ta hanyar tabbatar da canja yadda ake mulkar mutane a kasar nan, a kawo ci gaba ta hanyar watsi da Jari-Hujja.