✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mukan tara miliyan a kowanne wata – Jami’in LASTMA na bogi

Ya ce a kullum sukan iya tara N35,000

Wani magidanci mai shekara 55 da aka kama yana sojan gona a matsayin jami’in Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA), ya ce da shi da yaransa, sukan tara kimanin Naira miliyan daya a kowanne wata.

Jami’an hukumar ne suka kama mutumin a Ikoyi a karshen mako.

Ya ce ya shafe tsawon lokaci suna harkar a Jihar, kuma shi da yaran nasa sukan sanya riga mai daukar idanu, rubuce da sunan LASTMA a ciki.

Mutumin, wanda dan asalin Jihar Ondo ne, ya ce, “Ina zaune ne a gidan wani kanena da ke wani barikin sojoji a Legas.

“Nakan yi harkokina ne a wuraren Ikoyi da Obalende da gadar Apongbon da Iporin da kuma Olowu. Nakan kama motocin haya da na gida idan suka karya dokokin ababen hawa, ciki har da masu bin hannun da ba nasu ba.

“Ni da yarana mukan samu kusan Naira dubu 35 a kullum, muna kama mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

“Duk mai motar da muka kama ya ajiye fasinja a wajen da bai kamata ba, mukan caje shi N15,000 zuwa N20,000, wadanda kuma sukan karya dokar tuki kuma mukan karbi N35,000 a wajensu.”  in ji shi.

Shugaban hukumar ta LASTMA, Bolaji Oreagba, ya ce an kama mutumin ne a kan titin Olu Holloway da ke Ikoyi, kuma jami’an sintiri na hukumar da ke karkashin Ashafa Moyosore ya jagoranta.