✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mukabala: An bai wa Abduljabbar damar kare kansa —Kwamishina

Kwamishinan ya ce Abduljabbar ya kasa gabatar da litattafan da yazo da su wajen mukabalar.

Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano, Dokta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible), ya ce gwamnati ce ke da hurumin yanke hukunci game da mukabalar da aka gudanar tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano.

Kwamishinan ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala mukabalar wadda aka gudanar ranar Asabar.

  1. Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako
  2. Yadda barayi suka addabi majinyata a asibitin Gombe

“Yanzu za mu hadu da Gwamna gaba da gaba mu ba shi rahoto a rubuce, sannan ra’ayin gwamnati ne ta dauki mataki, amma ni a matsayina na kwamishina ba zan ce ga abin da za a yi ba.

“Ba a ba ni umarnin bayyana hukuncin da za a yanke ba, amma an yi mukabala lafiya an tashi lafiya, ba wanda aka tozarta ba wanda aka ciwa mutunci.

Kazalika, kwamishinan ya musanta korafin da Abduljabbar ya yi cewa ba a ba shi jadawalin yadda mukabalar za ta kasance ba.

‘A jira hukuncin gwamnati’

“Shi ya nemi a ba shi dama, ba malaman ba ne suka nema; to wanda ya ce a yi kokawa ai sai da ya shirya.

“Kowa an ba shi lokacin da ya dace, misali su an ba su minti 10 shi ma an ba shi minti 10.

“Tambaya ce guda daya, ka ce kaza sai ya nuna shafi da babi a littafin da ya gano abin da yake fada.

“Duk litattafan da ya zo da su babu guda daya da ya nuna, don haka ba laifinmu ba ne,” inji Kwamishinan.

Sai dai Abduljabbar ya nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da mukabalar, inda ya bukaci a sake saka lokaci don yin wata a nan gaba.

“A cikin rahoton da za mu bai wa gwamnati za mu rubuta bukatarsa ta son sake yin wata mukabalar, amma mu an turo mu shirya mukabala kuma mun aiwatar an yi lafiya an tashi lafiya, alhamdulillah,” inji Baba Impossible.

Ya kuma ce jama’a sun ga yadda mukabalar ta kaya, don haka za a jira hukuncin gwamnatin Jihar Kano, a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.