Dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Karbar Korafe-korafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya sami tikitin tsayawa takarar Sanatan Kano ta Arewa a karkashin jam’iyar PDP.
Hakan ya biyo bayan janye takarar Gwamnan Kano da yake yi tun da farko, kamar yadda ya shaida wa Aminiya.
- Jonathan zai iya sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023 — Kotu
- 2023: Tsohon Babban Hafsan Sojin Sama ne zai yi wa APC takarar Gwamna a Bauchi
Ya kuma ce magoya bayansa da masu ruwa da tsaki na jam’iyar ne suka shawarce shi da hakan, domin a cewarsa sun ga cancantarsa da kujerar a jam’iyar.
Muhuyi dai wanda ke ’yan gaba-gaba a masu zawarcin kujerar Gwamnan Kano a PDP ya kasance a tsagin jam’iyar na Ambasada Aminu Wali, da Bello Hayatu Gwarzo ke jagoranta.
Duk da zaben fid da gwani na PDPn da tsagin Gwarzon suka yi bai kammala ba har a safiyar ranar Alhamis, wanda tsagin shugaban iam’iyar da kotu ta tabbatar, Shehu Sagagi, suka gudanar ya tabbatar da Muhammad Abacha, da ga marigayi tsohon Shugabanci mulkin soja na Najeriya a matsayin halastaccen dan takarar Gwamnan jam’iyar.
Zaben bangarorin biyu dai na fid da gwanin ya samar da ‘yan takara biyu ga kujerar Sanatan Kano ta tsakiya kawai, yayin da ta Kano ta Arewa da kudu take ba kowa.