✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin tsaron kasa ga al’umma

1.Tsaron kasa babban nauyi ne da ya rataya a kan kowace gwamnati da ke kan mulki , ta yadda za ta dauki nauyin al’umma a…

1.Tsaron kasa babban nauyi ne da ya rataya a kan kowace gwamnati da ke kan mulki , ta yadda za ta dauki nauyin al’umma a kowane bagire na rayuwa. Tsaron kasa yana da ma’ana mai fadi kwarai. Jin dadin jama’a ta hanyar gudanar da al’adunsu da sanao’ insu da sauran shirye-shiryen rayuwa ba tare da tsangwama ba, alama ce ta kyakykyawan tsaro a kasa. Samun wannan kwanciyar hankali ba tare da tsoron kawo hari daga wani wuri ba, zai sa kasa ta ci gaba, musamman ta fuskar tattalin arziki da ciniki da ilimi da fasaha da kimiyya, wadanda da su ake tafiyar da harkokin duniya ga baki daya a halin yanzu.

2.Idan anyi maganar tsaro, akasarin jama’a su kan dauki fahimtar tsari na daga kawo hari daga waje. Wannan haka ne, amma kuma a cikin kasa ma akwai matsaloli da dama wadanda sukan janyo babbar baraka ga sha’anin tsaro. Rikice-rikicen siyasa da addini da kabilanci da rigimar ‘yan kungiyar kwadago da ‘yan jami’a, misalai ne na abubuwan da suke kawo barakar tsaro. Baki da ke zuwa kasar nan su zauna tare da mu, wadansu su shiga sace-sace ko manakisa da dabarun da za su sa sha gaban mu yaki da sauri, ta satar asirin kasa da ingiza hargitsi da husuma, har ma da tarzoma, karin misalai ne akan hanyar da ake samun barakar tsaro.
3.Saboda a dada tabbatar da lafiyar jama’a da kuma jin dadin su ne, gwamnati ta kafa hukumomin tsaro iri-iri a kasa. Sojoji da ‘yan sanda da kwastan da ma’aikatar shige da fice(Immigration) da Hukumar gidajen yari (Prisons) da makamantansu. Sauran sun hada da SSS da NIA da NDLEA da NAFDAC da EFCC da FRSC da NSCDC, wadannan sababbi ne a harkar tsaro. Ga bayanin ayyukansu dalla-dalla:-
A.Hukumar Tsaron cikin kasa (SSS)
4.Wanan ita ce hukumar tsaro ta cikin gida. Tana da rassa a ko’ina a jihohi da kananan hukumomi. Babban ofishinta yana Abuja. Harkokin da suka shafi sharri da kalamu marasa dadi da tushe don a janyo wa gwamnati bakin jini koma a tunkudeta da barna da tattalin arzikin kasa da kona kayan gwamnati da tarzoma da satar asirin gwamnati da dai laifuffuka manya, suna cikin ayyukan da hukumar ke kula da su, don ta tabbatar ba su faru ba. Babban aikin wannan hukuma dai shi ne ta hango manyan laifuffuka ta hanyar bincike ta kuma hana faruwarsu. Aikin hukumar ya yi kama kwarai da na hukumar ’yan sanda ba don yawan ‘yan sandan da karfin tabbatar da zaman lafiya wanda doka ta ba su ba.
5.Dokar soja da ta kafa Hukumar Tsaron Cikin kasa ta ba ta ikon daukar matakan da suka dace, wadanda dokokin kasa suka yarda da su wajen gudanar da bincike da kama mutanen da suke da laifi, domin a gurfanar da su a kotuna don a yi hukunci. Haka ma hukumar tana da shirye shirye da tsare-tsare, wadanda za su ba ta damar cimma burin tafiyar da ayyukan ta cikin nasara. Ma’aikatanta suna samun horon da ya dace da matsalolin ayyukan hukumar.

Hukumar tara bayanan tsaro a kasashen waje (NIA)
6.Ita kuma hukuma ce ta tsaro da ke kula da laifuffuka da ake yi wa Najeriya a kasashen waje. Idan an samu wasu suna buga kudin jabu don su shigo da su kasa, aiko da gurbatattun magunguna kasar nan, domin a yi wa mutanen mu illa da daukar sojojin haya don su kawo hari ko bai wa mutanen Najeriya horo irin na soja don kawar da gwamnati ko yin amfani da fasfo (paspot) na Najeriya don a boye suna, a yi zamba, a bata sunan kasa da dai abubuwa marasa kyau da ‘yan Najeriya za su iya yi kamar sace-sace, shigo da kayan fada, suna cikin ayyukan wannan hukuma. Muhimman bayanan duniya da suka shafi fasaha da kimiyya da siyasa da tattalin arziki da rikice-rikice na yaki, al’amura ne da hukumar ke bin kadinsu. Akwai ma’aikatan ta a ko’ina a duniya da suke kula da wadannan harkoki don a sanar da gwamnati idan sun faru.
B.Hukumar Tattara Bayanan Tsaro (DIA):
7.Itama wannan hukuma ce ta sojoji, wacce ke kula da tsaro. Ta na aikawa da mutanen ta kasashen waje don su tatttara bayanai kan al’amuran da ke faruwa a duniya na harkokin tsaro, wadanda suka hada da sababbin makamai da aka kera da dai samun ci gaba ta hanyar kimiyya da dabarun yaki. Maganar canjin mulki da bore akan shirya a waje, idan an gama shirin sai kuma a kawo shi gida a gudanar. Wannan hukuma tana kula sosai da irin wadannan al’amura. Ma’aikatan hukumar a gida da waje sun hada da farar hula da sojoji.
C.Hukumar tara Bayanan Sirri ta Soja (DMI):
8.Wannan hukumar ta sojoji ce. Tana kula da halaryarsu ga baki daya domin a tabbatar da babu wata baraka ta tsaro. Hukumar ta kasu gida uku. Da akwai bangaren sojojin kasa, na ruwa da na sama. Kowacce akwai tsarin da take bi kuma shugabannin su kan hadu su daidaita matakan tsaro da za a gudanar a bisa labaran da ake samu. Sojoji duka ko da ba su cikin hukumar tara bayanan sirri, hukumomi ne na tsaro, musamman ma wurin kare kasa daga hari da kasashen waje za su iya kawowa. A kullum a shirye suke wurin samun horo na dabarun yaki don kare kasa.
D.Hukumar Yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi (NDLEA):
9.Ita wannan hukumar aikin ta ta tabbatar ba a shigo da miyagun kwayoyi da kayan maye da ke cutar da jama’a. Haka ma tana da hakkin tabbatar ba a shuka su a kasa ba.
E.Hukumar Hana Fasakwauri ta Kwastam (NCS):
10.Hukumar kwastam dai an santa sosai. Babban aikinta shi ne samar wa kasa haraji akan kaya da ake shigowa da su cikin Najeriya. Hakkin hukumar ne ta hana fasakwauri da tabbatar da kayan da gwamnati ba ta yarda a shigo da su kasa ba. Akwai kayan ma da ba a yarda a fitar da su waje ba, wadanda hakkin wannan hukumar ta tabbatar ba ayi hakan ba.
F.Hukumar Shige da Fice (NIS):
11.Hukumar tana kula da shigowar baki cikin Najeriya da zaman su da iznin da aka ba su, su yi aiki wurin kyautata tattalin arzikin kasa. Tafiyar ’yan Najeriya zuwa kasashen waje da dawowar su, aikin wannan hukuma ne ta kula da alkaluman lissafi.

G.Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya (NPS) :
12.Hukumar tana kula da ‘yan kasa da ma na waje, wadanda suka yi wa kasa laifi, aka kuma daure su. Koya musu sana’a da kuma gyara halinsu, don a tabbatar horon da aka yi ya amfane su, hakkin wannan hukumar ne. Kebence masu laifi ga jama’a babban aikin tsaro ne, domin samun zaman lafiya a kasa.
H.Hukumar Tantance Ingancin magunguna da abinci:
13.Wanan hukuma tana kula da magunguna, ita ma wanda ake yi a kasa, don ta tabbatar masu kyau ne, a kare jama’a da amfani da magungunan jabu, a tabbatar da darajar su da karfin aikin su ba su nakasa ba. Ba ma maganin kadai ba, har ma abinci da abin sha kamar su burodi da ruwa, wannan hukumar tana tabbatar da kyawunsu kafin a sayar wa jama’a. Ita ce hukumar da ke bada da iznin sayar da ruwan sha bayan ta yi nazari da na’am da hannyoyin tattace shi.

I.Hukumar Yaki da yi wa Tattalin arziki Ta’annati (EFCC):
14.Wannan hukuma tana kula da zamba da rashin gaskiya da mutane ke yi, inda suke bata sunan kasar nan. Ta kan yi bincike, sannan ta kai masu laifi kotu don a hukunta su.
J.Hukumar Tsaron Farin Kaya (National Security Cibil Defense Corps):
15.Muhimmancin tsaro shi ne a samu zaman lafiya da walwala. Wannan hukumar an kafa ta ne da niyyar tallafa wa tsaro ta hanyar koyarwa da taimaka wa jama’a matakan da za su dauka don tsira daga hadurran da za su iya jawo mutuwa. An kafata ne lokacin yakin Biafra sannan daga baya aka gyara ayyukan ta, don kula da hana lalata bututun man fetur da aka shimfida a garuruwa, domin aikawa da man daga matatar Warri da Fatakwal da Kaduna. Aikin hukumar ya karu da ikon da aka ba ta na taimako wurin ceton wadanda gobara ko ambaliyar ruwa da sauran hadurran rayuwa suka yi wa illa. Hakkin hukumar ne ta koya wa kamfanoni tsare-tsaren tsaro na zamani, domin rage munanan ayyuka da suke kawo cikas a tsaron kasa.
K.Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC):
16.Aikin wannan hukuma yana da muhimmanci ainun akan tabbatar da tsaro akan hanyoyin sufuri na kasa. Aikin hukumar ne su tabbatar motoci suna tafiya cikin nutsuwa ba tare da gudun da zai kawo hadari ba. Hukumar ta hana daukar kayan sufuri da ya yi wa mota yawa, ta kuma tabbatar da motocin suna da lafiyar hawa titi. Hakkin hukumar ce ke kula da hadari da taimaka wa wadanda suka yi hadari zuwa asibiti don magani.
L.Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS):
17.Wannan hukuma aikinta kai dauki a wurin da gobara ta tashi, domin a kashe wutar cikin hanzari don kada a bar ta, ta yi barna a lalata dukiya koma a rasa rayuka. Yaki da wuta babban mataki ne na tsaro wurin kare jama’a da abubuwan da suka mallaka.

M. Sauran Hukumomin Tsaro:
18.A fahimci cewar dukkan ma’aikata ko hukuma da Gwamnati ta tsakiya, jiha ko karamar hukuma suka kafa domin tsaron lafiya da jin dadin jama’a, wannan ma’aikatar ta shiga layin hukumomin tsaro. Bambancin kawai na irin dokar da ta kafata ne da irin aiyyukan da za ta yi. Hukumar kashe gobara da Hisbah da Karota da ‘yan kato dagora, wadanda doka ta kafa, hukumomin tsaro ne. Ko an ba su damar daukar makamai, ko ba a ba su ba, in dai za su dauki matakan zama lafiya da tallafa wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro, darajarsu su ma ta masu kula da tsaron ne.
N.Na’urorin fasaha da Kimiyya da Sadarwa:
19.Duk wadannan matakai da Gwamnati take dauka wurin kafa hukumomi daban-daban, don kyautata rayuwar jama’a wajenn samar da zaman lafiya, wanda zai kawo ci gaba. Duniya yanzu ta zama dan karamin wuri, duk abubuwa da suke faruwa kowa ya sani, ta hanyoyin sadarwa kamar telebijin da kwamfuta. Akwai na’urorin fasaha da dama da ake amfani da su wajen sadarwa, ta hanyar aikawa da sakonni ko’ina a duniya. Yanar gizo-gizo ta kwamfuta da wayoyin hannu da sauran na’urorin sadarwa suna da muhimmanci kwarai ga ma’aikatan tsaro wajen tattarak bayanai masu amfani. Wayoyin hannu sukan dauki hotuna na abubuwan da suke faruwa, kuma su aika inda suke so cikin hanzari. Za su iya daukar maganganu da ake yin su, a ajiye domin kafa shaida na abubuwa da suke sha’awa a ciki. Wayar da ake amfani da ita, za ta iya bada taswirar inda mai rike da itada cikakken bayanin inda mai amfani da ita yake, watau “global positioning system” a Turanci. Akwai bukatar kame kai daga subul da baka akan harkoki ko matsalolin da suka shafi tsaron kasa akan wadanda hukuma tsaro za ta nemi karin bayani, domin a kare lafiyar jama’a.
20.Duk ingantaccen labarin da ake samu, akan tattace su, sannan a mika wa masu mulki domin su yi amfani dasu wurin tsare-tsare da suke so suyi don kyautata rayuwar jama’a. Idan labarin da aka samu ya nuna hadari ko kuma jama’a ba za su yi na’am da shi ba, masu mulki sukan yi tunanin su zabi abin da zai fi dacewa jama’ar. Maganar tsaro sabo da haka mu’amala ce wacce ta shafi kowa. Samun nasarar ta kuwa sai kowa ya taimaka da gudunmawa, na ba da hada kai wajen gudanar da abubuwan da Gwamnati take yi domin kwanciyar hankalin jama’a.

Zargin masu aikin tsaro
21.Akwai zargi sau da dama da ake yi wa masu aikin tsaro akan sharri ko kage. Hukumar tsaro ko kadan ba ta yarda da hakan ba. Ma’aikatan da aka samu ba su da gaskiya da rikon amana a wurin tafiyar da aikinsu akan hukunta su, kuma a sallame su daga aikin. Dadin tsarin shi ne za a kai mai laifi kotu, inda za a ba shi dama ya kare kansa a laifin da aka ce ya yi. Don kasa da yake harkokinsa akan ka’idodi na zaman lafiya babu wanda zai lakaya masa laifi. Zargi na kamawa idan an samu baraka wurin yin abubuwa ba daidai ba. Irin wanan zato maras tushe ya zame wa maaikatain tsaro jiki kuma sun dauke shi a sadaukar da kai da suke yi wurin bautawa kasa domin a sami zaman lafiya da jin dadin jamaa.
P: Aikin tsaro a zahiri da asirce:
22.Kafin a kafa hukumomin tsaron da aka ambata, a da can ‘yan sanda (Police) ne kadai ske kula da harkokin tsaro. Bayan kashe Janar Murtala Muhammed a 1976, aka kafa Nigerian Security Organisation (NSO), don ta kara kula da harkokin tsaro. A 1986 ita (NSO) din ma aka gyarata, ta haifi hukumomin tsaro da suka hada da SSS da NIA da DIA. Amma kuma wajibi ne a fahimci cewar dukkan harkokin tsaro na zahiri da zaman lafiyar jama’a na ‘yan sanda ne ba ma a Najeriya kadai ba, ko’ina a duniya. Kundin tsarin mulkin kasa ma ya tabbatar da haka. Saboda kula da doka ne ma yasa aka yi musu lakabin ‘yan doka. Ci gaba da aka samu na rayuwa ya kawo canje-canje domin a tallafa musu.
Ofishin Mai bayar da shawara kan tsaron kasa:
23. daukacin rahoton tsaro ana aikawa da su ofishin Shugaban kasa, a wurin mai bai wa Shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro. Idan akwai bukata, Shugaban kasa ya kan kirawo taron majalisar tsaro, wacce ta kunshi Ministocin Tsaro, Cikin Gida da Jami’an Tsaro na Sojoji duka, Babban Jami’in ‘Yan sanda da Shugabannin Hukumomin Tsaro na Cikin Gida da na Waje, domin su tattauna a zartar da matakan da suka dace. Daga nan kuma za a aika wa sauran ma’aikatu da umarnin abin da ake son su yi don gudanar da abubuwa da aka zartar.
k: Ta’addancin da ya addabi kasa:
24.Bai kamata a ce bayanin da ake yi akan manufofin sahihin tsaro na kasa ya samu tangarda da shakku a wurin jama’a ba. Tangardar ita ce akwai ‘yan ta’adda da masu tsaron kasa ke fada da su fiye da shekara uku ba da kyakykyawar nasara ba. Salon fadanne ya bambanta da wanda aka saba, kuma akwai rashin isassun kayan fadan, wadanda gwamnati ta dukufa wurin samowa. Babu mamaki ma idan akwai hannun kasashen waje, wadanda ta dabaru irin nasu suke taimaka wa ‘yan ta’addar, domin kasar mu ta ruguje, Allah ya kiyaye. Gwamnati tana kara shiri wajen amfani da jiragen sama da miyagun makamai, domin a dakile ta’addacin da lalata dukiyar jama’a da asarar rayuka. A ci gaba da yi wa masu tsaron kasa addu’ar nasara wacce za ta kawo mana zaman lafiya.
R: karshen jawabi
25.A karshe ina so jama’a su fahimci muhimmancin tsaro, wanda sai an same shi ne za a sami zaman lafiya mai karko, wanda zai kawo ci gaba. Burin mu na gudanar da harkokin mu, da suka hada da ciniki da addini da sauran tsare-tsare na rayuwa, ba za su samu nasara ba idan babu kyakykyawan tsaro. Mu zauna lafiya da makwaftanmu ba tare da shayin ko tsoron za a kawo mana hari ba, sai muna da tsarin tsaro mai inganci. Mu’amala da muke yi da kasashen waje, da sunan da muka samu na shugabancin kasashen Afirka, da arziki da Allah ya ba mu na ma’adinai da mai da al’umma masu hazaka, suna bukatar tsaro da za a amince da shi, wanda zai ba mu karfin zuciyar tafiyar da harkokin sosai.
26. A taimaka da bai wa hukumomin tsaro shawarwari na amana akan abubuwan da ake ganin za su kawo barakar tsaro, domin a dauki matakin da ya dace da sauri don samun zaman lafiya. Kada a bai wa abokan gabar mu dama su dawo da ci gaban mu baya. Ya wajaba ga jama’a duka su yi hobbasa wurin ba da gudunmawa akan matsalolin tsaro. Cikin ikonsu ne gwamnati ke daukar matakan da suka dace, kamar yadda zaben jama’a ya ba ta dama. Allah ya kara mana ci gaba a Najeriya.
A tuna cewar doka ta dora wa shugabannin jama’a wajibcin sana’ar da hukumomin tsaro labarin aukuwar wani abu da zai iya cutar da jama’a, domin a gudanar da bincike cikin lokaci da daukar matakan da suka dace wurin kau da illar da za ta shafi jama’a. An tanadi horo mai tsanani akan jami’an mulki da aka same su da sakacin yin hakan. Allah Ya ba mu sa a da rayuwa mai kyau. Amin.
(Amb B.M. Sani, mni), Sharada kuarters, [email protected] 08035902069.