✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin kwalliya ga mata

Kwalliya dai ta hada da tsaftace jiki, sanya tufafi masu kyau, gyaran fuska, da sauransu. Mutane kan yi kwalliya ne domin su ji dadin jikinsu…

Kwalliya dai ta hada da tsaftace jiki, sanya tufafi masu kyau, gyaran fuska, da sauransu. Mutane kan yi kwalliya ne domin su ji dadin jikinsu kuma su burge wasu. Mata akafi sani da ado. Duk duniya duk inda aka ce ga wata mace to za a yi tsammanin ganin ta caba ado da kuma yin kwalliya, musamman ma idan aka ce wajen wani taro ne walau na biki ko suna ko kuma wani sha’ani. Haka ma a al’adar Hausawa, an dauki kwalliya da yin ado ga ’ya mace da matukar muhimmanci.   Shi ya sa Hausawa kan yi wata karin magana da: “Mata adon gari”. 

Kwalliya na da muhimmanci ga ’ya mace domin ya kasance tamkar shi ne jarinta.  Kwalliya na kara wa mace kima da daraja a idon jama’a.  Muddin mace ta kasance kullum cikin datti, da rashin kwalliya, za ki ga darajarta da kuma kimarta ya ragu a idon jama’a ko da a cikin gidansu ne.

Bugu da kari, kwalliya kan sa mace ta zama ’yar lele abin kauna a wajen mijinta ma matan aure, kamar yadda kwalliya kan janyo hankalin maza su rika yin rububi a kan budurwa kafin ta yi aure.  Burin kowane namiji ne ya auri mace mai tsafta da kwalliya.  Sai ki j wasu mata na mitar cewa mazajensu ba su cika son komawa gida da wuri ba, amma ba su sani ba watakila saboda rashin tsafta da kuma yin kwalliya ba ne.  Wane namiji ne zai so ya koma gida ya tarar da matarsa da kuma gidansu cikin datti.  Wasu matan za ka tarar hatta yaransu sun kasance cikin dauda hancin duk majina ita kanta matarsa cikin kazanta ga harabar gidan ya yi kaca-kaca da bola da kazanta.  Ga kwanonin girki birjik kudaje na bi ba a wanke ba. 

Da maigida zai dawo gida ya tarar uwargida ta yi wanka ta caba ado, ta kintsa ko’ina ta shirya ’ya’yanta ta hada masa girki mai rai da lafiya, ko’ina cikin gidan sai daukar kamshi yake yi, me kike zato, ai da zarar ya tashi daga ofis ko kasuwa, hankalinsa zai koma gida ne don ya san zai koma wajen da zai samu farin ciki da kwandiyar hankali ne.  Babu namijin da bai son ya ji dadi ko ya kasance a wuri mai kyau.  Duk kazantar namiji ba zai so ya auri mace kazama ba, don haka wannan darasi da na dauko tamkar kalubale ne ga mata.  Masu gulma da irin wannan mace suna cewa ta shiga bokaye wajen mallakar mijinta, to sun tafka kuskure.

A gaskiya kura-kuraen da mafi yawa daga cikin mata shi ne yadda ba sa yin kwalliya sai za a fita anguwa.  Akwai matar da mijinta bai taba ganin kwalliyarta ba, don ba ta yin kwalliya idan ya kasance yana gida, sai za ta tafi unguwa.

Idan tana gida, za ka tarar tana cikin tsumma ne mai dauke da datti yana wari, ba ta damu da gyara jikinta ba, wata ma ko kitso ba ta yi sai ya shafe wata da watanni, amma wai a haka take bukatar mijinta ya rika kusantarta. Mata su sani sirrin mallakar gida yana cikin kwalliya ne da iya caba wa maigida ado.  Duk macen da ta iya yin kwalliya, ko shakka babu za ta mallake zuciyar maigidanta ko da su hudu ne a gidan. Za ka tarar mijin nasu ya fi ba ta kulawa ta musamman.

Mata ma masu abokan zama, ya kamata ku tashi tsaye wajen yin kwalliya da tsaftace muhalli. Ba Boka ba shiga Malam, da kwalliya kadai za ki mallake mijinki. Za ki kasance ba raini, ba wulakanci a gidan miji. 

Ita kwalliya fa ba sai matan aure kadai ba, kwalliya na da matukar muhimmanci ga ‘yam mata. Kwalliya za ta sa ki fita daban a cikin kawayen ki. ’Yan mata da dama na yin kwalliya domin yana kara musu kwarjini da daukaka a duk inda suka kasance. Kuma burin kowace mace ta kasance a gidan mijinta. Ki sani cewa babu wanda yakeso ya auri mace kazama.  Kuma duk abun da za ki yi a gidan miji tun a gida za ki koya.

Mu sani cewa babu mummunar mace sai wacce ta yi sake . Duk yadda halittar ki take, ya rage naki ne sanin yadda za ki kawata ta da abubuwan da za su dace da ita. Mu rika yin kokari wajen gyara jikinmu domin kare kimarmu a idon jama’a. Ke kan ki za ki fi jin dadin jikinki idan ya yi kyau.

Da fatan za mu dauki darasi daga wannan dan fadakarwa da na yi musamman ga ’yan uwana mata.