✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin dariya ga lafiya

Mutane na dariya a lokacin da suke nishadi. Mutane duk duniya na yin dariya. Ita dariya ba ta da yare kuma ba ta da kabila.…

Mutane na dariya a lokacin da suke nishadi. Mutane duk duniya na yin dariya. Ita dariya ba ta da yare kuma ba ta da kabila. Kowa na yinta. Amma mutane da dama ba su san amfanin dariyar ba. Dariya na da amfani sosai a jikin dan Adam.

Dariya na sa fuskar mutum ta kara kyau da lafiya har ma da yarinta.

Bugu da kari, dariya na kara garkuwar jiki wajen yaki da cututtuka. Idan mutum ya yi dariya, akwai wani sinadari da ke fita a jikin mutum idan yana dariya, wanda yake taimakawa wajen yaki da cututtuka.

Hawan jini da ciwon suga duk suna raguwa idan mutum yana dariya. Bincike ya nuna cewa wadanda suka kalli wasa mai ban dariya bayan cin abinci yawan sukarin jininsu bai kai na wadanda suka kalli wasan da bai da abin dariya ba.

Wani abu kuma da dariya take yi shi ne sa bacci mai dadi. Yin dariya kafin bacci na rage gajiya da damuwa, hakan na sa mutum ya yi mikakken bacci mai dadin gaske.