✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimmancin amfani da sukari a fata

Asalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin filinmu na kwalliya. Na san za a yi mamaki idan na ce amfani da sukari a fatar…

Asalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin filinmu na kwalliya.

Na san za a yi mamaki idan na ce amfani da sukari a fatar jikinmu na da matukar muhimmanci.

Yanzu zamani ya kawo mu inda mace ba sai ta shiga kasuwa domin neman nau’o’in man gyaran fata ba, daga cikin kicin ma za a iya hada wasu abubuwa da za su magance matsalolin fata.

Don haka ne a yau na kawo muku muhimmancin amfani da sukari a fatar jiki. A sha karatu lafiya.

  • Domin samun lebba masu sulbi, a zuba ruwa kadan sosai a cikin sukari yadda ruwan ba zai narkar da shi ba, sannan a riqa murza lebban da wannan hadin sukarin domin samun fatar lebba mai sulbi.
  • Za a iya yin dilka da sukari. A samu sukari mai ruwan kasa sannan a kwaba shi da ayaba sai a rika dirzawa a fatar jiki domin cire matacciyar fatar jiki da kuma samun sabuwar fata mai haske.
  • Idan ana buqatar samun shekin fata a kafa da wuya da baya, sai a kwaba sukari da man kwakwa ko man zaitun sannan a dage da dirza waxannan bangarorin jikin da na lissafo akalla sau biyu a mako domin samun fata mai sheki a wadannan bangarori.
  • Sukari na magance gautsin tafin kafa ko faso ko kauje.

A kwaba sukari da man kwakwa sannan a zuba a roba sai a saka tafin kafa a ciki a rika dirza tafin kafar na tsawon minti 10 zuwa 15 domin magance matsalolin kauje ko faso a fata.

  • Idan an kasance ana da gautsin fatar tafin hannu, sai a rika gauraya sukari da sabulu ana dirzawa a hannu sannan a wanke domin samun fata mai laushi.
  • Domin rabuwa da gashin kafa, sai a samu sakari mai ruwan kasa, a kwaba da ruwa kadan sai a shiga murza fatar kafa sannan a sanya reza a cire gashin kafa.

Maza masu fama da cututtukan fata idan sun aske gemunsu za su iya amfani da irin wannan hadi domin samun saukin aske gashin baki.

  • Za a iya amfani da man zaitun da sukari mai ruwan kasa sannan a kwaba a rika shafawa a fatar hannu kafin a shiga wanka. Yin hakan na sanya fatar sheki da laushi da sulbi.