✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmanci da kuma tasirin daidaita sahun sallah (2

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Muhammadu…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa har zuwa ranar sakamako. 

Bayan haka, yau ga ci gaba, kuma karashen mukalar muhimmanci da tasirin daidaita sahu. Mun kwana a daidai inda mukalar ta ce:

Dagainaakefarasahu?
A sunna dai, a sallarjama’a (jam’i), ana fara kafa sahun farko ne a (daidai) bayan liman, sai (sahun) ya bazu zuwa gefen damarsa (shiliman), sannan sai gefen hagunsa. Haka abin yake (kasancewa) a sahu na biyu, sai na uku, …har zuwa karshen dukan sahun da ya samu (ko zaisamu). Saba wa wannan tsari, (na yin sahu-sahu), ana kirga shi cikin bidi’a (kirkira), saboda ya saba wa karantarwar Annabi, sallallahu alaihi wasallam. Wannan kuwa haka al’amari yake saboda hadisin Abiy Hurairata, Allah Ya yarda da shi, ya nuna cewa, Ma’aikin Allah, sallallahu alaihi wasallam, ya ce, “Ku tsakiyanci liman, kuma ku rurrufe kafafe.” Abu Dawuda ya ruwaitoshi.
Idan mamu (mabiya sallah) suka tsakiyanci liman, sai sahu ya mika zuwa dama, kamar yadda hadisin A’ishatu, Allah Ya yarda da ita, ya nuna, cewa ita ta ce, Manzon Allah, sallallahu alaihi wasallam, ya ce, “Lallai Allah da mala’ikun Sa suna salati ga damammakin sahu.” Abu Dawuda ya fitar da shi da isnadin da ke kan sharadin Muslim. Manufa a nan ita ce ana sunnanta, idanmamu ya isa masallaci ya sami mutane sun tsakiyanta liman, watau sun bazu a bayansa (dama da hagu), sai ya ga wata kafa a daman liman da kuma wata kafar a hagunsa, (abin da ke sunnar shi ce) sai ya rufe kafar da take (gefen) dama (tukun, ya bar kafar da take gefenhagunsa). Amma kuma kada lizimtar kwadayin falalar dama ta haifar da kubucewar sunnar tsakiyancin liman (watau bazuwa dama da hagu a bayansa) wanda ake bukatar kasancewarsa. Muhallin neman damantawa (wanda ake nufi) shi ne idan gefensa yana wadatar duk an ma zo wa masallacin (ko wurin sallar), in ba haka ba kuwa, to sai dai a yi tseren zuwa wajen, in ya cika shi ke nan, sai saura su yi sallah a hagun liman. Wannan magana Muhammadu dan Allaan Assidiik, wanda ya yi littafin Dalilul Falihina ne ya fade ta (a littafin nasa).

Ya ya ake daidaita sahu?
To, amma yadda ake daidaita sahu, lallai da yawa daga cikin masallata, kowa na tsayawa yadda ya so ne a cikinsa (sahun), kuma da yawasuna kudurce cewa daidaita sahu ya na isa da hada gefen ’yan yatsun kafa; wannan kuwa saba wa sunna ne. Sunna tabbatacciya a cikin haka ita ce sadar da duga-dugai da kafadu. Yana daga cikin tabbatuwar haka, hadisin Nu’umanu dan Bashir, Allah Ya yarda da su, ya ce, “Ma’aikin Allah, sallallahu alaihiwasallam, ya fuskantomutane, sai ya ce, ‘Ku tsayar da sahunku (ku daidaita shi)’ – ya fadi haka sau uku – (sannan ya ce),‘Wallahi, ko dai ku tsayar da sahunku, ko kuma, wallahi, Allah Ya sassaba tsakanin zukatanku.” Nu’uman ya ce, “Sai in ga mutum ya sadaka fadarsa da kafa dara bokin tsayuwarsa, kuma da (gefen) gwiwarsa ya sadu da (gefen) gwiwarsa, kuma duddugensa da duddugensa.”
A cikin wannan hadisi akwai abin lura maigirma a cikin siffar yadda ake tsayuwa a cikin sallah.Yadda al’amari yakeshi ne duk wanda ya sada (gefen) gwiwarsa da ta dan uwansa da kuma duddugensa da na danuwansa, babu shakka ya kasance kafarsa ta tsayu sak ta fuskanci alkibla. Da wannan yanayi sai a samar da abin da ake nema na daidaituwar sahu. To, amma idan ya fuskantar da ita (kafar) ta fuskanci dama da hagu, sai saduwar karamin dan yatsan kafa ya sadu da na dan uwansa, a wata kafar, alhali irin wannan daidaituwa ba ita ce daidaituwar sahu ta sunna ba. Kuma a cikin yin hakan, babu wani hadisi mai rauni balle sahihi, wanda ya yi nuni da shi (balle ya goyi bayan hakan).
Lallai, babu shakka, Annabi, sallallahu alaihi wasallam ya ce, “Ku tsayar da sahunku, kuma kuma nan ne (sumunce) shi, na rantse da Wanda raina ke hannunSa, ni ina ganin shaidanu (sunashiga) a tsakanin sahunku, kamar dai su wasu ’yan kananan bisashe (dabbobi) ne.” Hakan kuma ya ce, “Ku daidaita sahunku, domin daidaitasahu yana daga cikin tsayar da sallah.”
Kai, (haka dai ake ta bayyana wahalar) da dai zuwa ga abin da ba wannan ba, na bayanan da suka gabata da wadanda ba a kawo ba, wadanda suka danganci manuniyar daidaita sahu da umurni a kan haka.Saboda haka lallai a bibiyi ilimin da ya danganci yadda ake daidaita sahun sallah don a samu dacewa da sunnah. Kai, ba sahu ba kawai, kowane irin aiki na ibada, wajibi ne a samu tabbataccen iliminsa, sannan a aiwatar da shi don samun kaiwa ga abin da ake nufi dangane da samun ladar aikin ibada, alhali an yi koyi da Manzon Allah, sallallahu alaihi wasallam, kuma a yi saboda Allah Shi kadai (ikhlasi). Allah Ya ba mu dacewa!
Wannan (bayani da ya gabata) shi ne dan takaitaccen abin da ya saukaka gareni in fitar don nasiha (da manuniya) ga al’ummar Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam, (domin) su tsayar da hakkin abin da ya umarta, alhali shi manzo ne na rahama da shiriya. Har ya kasance sun tsaya a kan tafarkin sammai haske, wanda darensa kamar ranarsa ne. Babu mai kauce mata (ita sunnar) face ya yinisa da basira da kuma hankali (watau sai mahaukaci ke waskewa daga shiriya). Kuma Allah Ta’ala dai nake (kara) roko ya sanya wannan aiki ya kebantu saboda da Shi kadai, don ZatinSa, Mai karimci… fa subhaanakallaahumma wa bi hamdika, ashhadu an la’ilaha illaa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika…(watau) kuma tsarki ya tabbatar maKa, ya Allah, tare da godiya gare Ka, ina shaida wa babu wanda ya cancanci a bauta wa (da cancanta) sai Kai kadai, ina neman gafararKa, kuma ina tuba gare Ka…. Allah Ka yi tsira da aminci da albarka ga bawanKa, manzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa, aminci mai yawa.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah!