✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman batutuwan da za su mamaye taron Shugabannin Afirka a Habasha

Yawan juyin mulki a nahiyar na cikin muhimman batutuwan da za su mamaye taron.

A ranar Asabar, Shugabannin kasashen Afirka sun fara taron kwana biyu na Kungiyar Hadin Kan Afirka ta AU karo na 35 a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Taron na kasashe 55 an fara shi ne a daidai lokacin da kungiyar ke fuskantar matsin lamba kan ta tilasta wa kasar da ke karbar bakuncinsa wato Habasha ta tsagaita wuta a yankin Tigray da ya shafe kusan wata 15 yana fama da rikici.

A gefe daya kuma, nahiyar a ’yan shekarun nan na fama da yawan yunkurin juyin mulki har sau shida a wata 18 din da suka gabata, musamman a wasu kasashen Afirka ta Yamma, kuma hakan na cikin manyan batutuwan da za su mamaye taron.

A daya bangaren kuma, har yanzu Afirka na ci gaba da fama da annobar COVID-19.

An dai kafa kungiyar ta AU ne shekaru 20 da suka gabata don bunkasa hadin kan kasashen nahiyar.

Tuni dai Kwamitin Tsaro na Kungiyar ya kori kasashe hudu daga kasancewa mambobinsa tun shekarar 2021, saboda fuskantar hambarar da gwamnatocin dimokuradiyya, inda ko a makon da ya gabata sai da aka hambarar da gwamnatin Christian Kabore a Burkina Faso.

Shugaba Buhari tare da tawagar Najeriya yayin taron
Shugaba Buhari tare da tawagar Najeriya yayin taron

Da yake jawabi ga Ministocin Harkokin Waje na nahiyar a wannan makon, Shugaban kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana yawan juyin mulkin a matsayin abin damuwa matuka.

Jiga-jigan Shugabannin kasashe a nahiyar irin su Najeriya da Senegal da Kenya ne suke halartar taron, kodayake akwai irin su Shugaba Yoweri Museveni na Uganda da ba za su samu halarta ba.

Ana sa ran taron na kwana biyu dai zai yi hobbasa wajen daukar tsauraran matakan da za su kawo karshen matsalar yawan juyin mulki a kai a kai a nahiyar.

Shugabannin za su kuma su duba batun hadin gwiwa a tsakaninsu tare duba yiwuwar aiki tare don magance matsalar tsaro da ke fuskantar sassa da dama na nahiyar.

Daga cikin kwafin batutuwan da za a tattauna a taron, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya gani, har da batun amincewar da Moussa Faki ya yi a bara da tantance Isra’ila a madadin AU.

Matakin dai a lokacin ya fuskanci zazzafan martani daga kasashe da dama masu karfin fada a ji a kungiyar, ciki har da Afirka ta Kudu da Algeria, wadanda suka ce ya saba da manufar AU ta goyon bayan Falasdinawa.