✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwan kwalliya

Mata da dama ba su san muhimman ababen yin kwalliya ba. Abubuwan da suka sani ba su wuce gazal da hoda da kuma jan baki…

Mata da dama ba su san muhimman ababen yin kwalliya ba. Abubuwan da suka sani ba su wuce gazal da hoda da kuma jan baki ba. Ana son ‘ya mace ta kasance mai yawan kwalliya da yin ado. Yin hakan zai inganta kimarta da kuma kyaunta. A yau zan kawo muku muhimman abubuwan kwalliya domin yakamata kowace ‘ya mace ta san su. Ba sai an ji wadansu na fada ba sai a yi kamar an sani, alhali ba a sanin ba.

· Amfanin ‘concealer’ ; idan ke ba mai yawan kwalliya ba ce bai kamata ki dauki hodar ‘concealer har ki shafa a fuskarki sai kin san yadda ake amfani da ita. Ana amfani da ita ce wajen boye wani dabbare-dabbare dake karkashin idanu da kuma samansu. Sai a shafa wannan domin ya boye wannan bakaken kala.
· Fandesho; ana amfani da shi ne domin inganta hodar da za a shafa. Kuma a tabbatar da cewa an samu wanda ya dace da fata kafini a shafa in ba h ka ba kwalliyar za ta lalace. Ana amfani da shi ne kuma domin haskaka fuska.

· Blush ; ana shafa shi ne a kumatu watau ‘taya ni muni’ kamar yadda ake fada. Amma ya fi wa fararen mata kyau.

· ‘Translucent powder’; ana amfani da ita ne wajen tsane maikon fuska a lokacin da ake kwalliya.

· ‘mascara’; ana amfani da shi ne domin taje gashin ido. Domin su yi tsawo kuma su yi kyau.

· ‘eye shadow’ ; ana amfani da shi ne domin shafa wani kala irin na kayan da aka sanya a fatar saman ido. Yin hakan kuma na kara inganta kwalliyar mace.