A wannan Alhamis ɗin aka shiga rana ta 174 da soma yaƙin da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza.
Yakin da Isra’ila ke yi da Falasdinawa a Gaza – wanda ke cikin kwana na 174 – ya kashe akalla mutane 32,490 tare da raunata 74,889, kamar yadda alƙaluman mahukunta suka tabbatar.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban bara ne aka soma yaƙi tsakanin dakarun sojin Isra’ila da mayaƙan Hamas a Zirin Gaza.
Yaƙin ya soma ne bayan wani harin ba-zata da Hamas ta kai wa Kudancin Isra’ila daga Zirin Gaza
Ga yadda abubuwa suke a ranar Alhamis, Maris 28, 2024:
A safiyar Alhamis ɗin nan ne tashar talabijin ta Aljazeera ɓangaren Larabci ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama a Arewacin Gaza, ciki har da birnin Gaza da sansanonin ’yan gudun hijira na Shati da Jabalia.
A waje guda kuma, faifan bidiyo da gidan talabijin na Aljazeera ya samu a ranar Alhamis ya nuna yadda sojojin Isra’ila ke harbin wasu Falasɗinawa biyu da ke tafiya a gaɓar tekun zuwa Arewacin Gaza. Wasu mutum biyu ‘yan Isra’ilawaɗanda suke ɗaga farin ƙyalle a daidai lokacin wata mobat katafila ta binne su.
Kusan Falasɗinawa 160 ne suka mutu yayin da 195 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila tsakanin ranakun Litinin zuwa Laraba, kamar yadda ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya OCHA ya bayyana a ranar Laraba.
Kashi biyu bisa uku na asibitocin 36 na Gaza “ba sa aiki” yayin da waɗanda suka kasance a buɗe ko dai “aƙalla kaɗan” ko ” wani ɓangare” suke aiki, a cewar OCHA.
Ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa ta Red Cross da Red Crescent Societies sun ruwaito a ranar Laraba cewa tsarin kiwon lafiya a Arewacin Gaza “an lalata shi sosai” kuma yana kan rushewa sosai a Kudu.
Za mu kai farmaki Rafah — Netanyahu
Kamfanin dillancin labaran Isra’ila ya rawaito cewa Firaminista Benyamin Netanyahu ya bayar da umarnin sayen tantuna 40,000 daga kasar China da za a kafa a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, a shirye-shiryen kai farmaki ta kasa a Rafah inda Falasdinawa sama da miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Netanyahu ya yi watsi da fargabar da duniya ke da shi na fuskantar bala’in jinƙai idan Isra’ila ta kai farmaki ta kasa a yankin kudancin Gaza, yana mai cewa fararen hula za su iya tserewa fadan zuwa wasu sassan yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Da yake magana da tawagar majalisar dokokin Amurka da ke ziyara a Isra’ila, Netanyahu ya ce mutanen da ke mafaka a Rafah – fiye da rabin al’ummar Gaza miliyan 2.3 – za su iya ficewa daga faɗan.
“Kawai mutane su tafi, su tafi da tantunansu,” in ji Netanyahu a cikin kalamansa na izgilanci. “Mutane sun koma Rafah. Suna iya sake barin can ɗin ma.”
Kutsen da Isra’ila ke shirin yi ya tayar da hankulan duniya saboda birnin, wanda ke kan iyakar Gaza da Masar yana cunkushe da Falasdinawa sama da miliyan 1.5 a sansanoni da tantuna da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wadanda galibinsu suka tsere daga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa wasu wurare.
Muna umartar Isra’ila ta dauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza — Kotun ICJ
Alkalai a kotun kasa da kasa baki dayansu sun bai wa Isra’ila umarnin daukar dukkanin matakan da suka dace kuma masu inganci don tabbatar da isar kayayyakin abinci na yau da kullun ga al’ummar Falasdinu a Gaza.
Kotun ta ICJ ta ce Falasdinawa a Gaza na fuskantar mummunan yanayi na rayuwa kuma yunwa da tsananin rashin abinci na yaduwa.
“Kotu ta lura cewa Falasdinawa a Gaza ba barazanar yunwa kawai suke fuskanta ba (…) mummunan fari ma ya kunno kai,” in ji alkalan a cikin umarninsu.
Kasar Afirka ta Kudu ce ta bukaci sabbin matakan a matsayin wani bangare na shari’ar da take ci gaba da yi na zargin Isra’ila da kisan kiyashin da take yi a Gaza.