Amurka ta jinjina wa wani likita dan Najeriya, kan rawar da ya taka wurin samar da rigakafin cutar COVID-19 da kamfain Pfizer ya hada.
Pfizer da BioNTech da suka yi rigakafin da Dokta Onyema Ogbuagu ya kirkiro sun ce shi ne aka fara samarwa na cutar COVID-19, kuma ya warkar da 90% na wadanda aka yi wa amfani da shi.
- Dan Najeriya ne ya kirkiro rigakafin COVID-19 a Amurka
- Dattijo ya nemi budurwa ta biya shi N50,000 saboda kin auren shi
- Dukan dan takara: Kotu ta sa a kamo Shugaban Karamar Hukumar Gaya
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, ya yaba wa kwazonsa wurin samar da rigakafin, “Ya bayar da gudunmawa mara misaltuwa na ganin an kawo karshen annobar da ta gallabi duniya”.
‘Yan Najeriya sun ba wa duniya gudunmuwa ta fuskoki da dama. Muna matukar jinjina ga Dokta Onyema Ogbuagu da ya taimaka aka samar da rigakafin COVID-19”, inji Ofishin.
Ofishin jakandancin ya sanar da haka ne ta shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Ingancin rigakafin Dokta Ogbuagu
Pfizer ya ce rigakafin Dokta Ogbuagu shi ne mafi inganci da aka fara samarwa na COVID-19 a duniya.
An yi gwajin allurar rigakafin a kan mutum 43,500 da suka kamu a kasashe shida kuma babu alamar ya ya haifar musu da barazanar lafiya.
Kamfanin Pfizer ya ce, zai samar da rigakafin guda miliyan 50 kafin karshen 2020, da kuma guda biliyan 1.3 zuwa karshen shekarar 2021.
Muhimman abubuwa 10 kan Dokta Ogbuagu
- Likita Ogbuagu shi ne ya jagoranci kwararun masu bincike kan samar da rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer.
- Katafaren kamfanin Pfizer, na daga cikin na gaba-gaba a fagen bincike da hada magunguna a duniya.
- Dokta Onyema ya yi digirinsa na farko ne a fannin aikin likita a Jami’ar Kalabar a shekarar 2003.
- Yanzu haka shi Farfesa ne a kimiyar magani da cuttuka masu yaduwa a Jami’ar Yale da ke Amurka.
- Mahaifinsa shi ne tsohon Shugaban Jami’ar Jihar Abia, Chibuzo Ogbuagu.
- Mahaiyarsa, Stella Ogbugau Farfesa ce a fannin Nazarin Halayyar Dan-adam.
- Ita ce wacce ta fi kwazo a daliban da Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta yaye a 1974, wadda ta kammala da digiri mai daraja ta daya.
- Bayan kammala karatunsa na aikin Likita a Jami’ar Kalaba a 2003, Dokta Ogbuagu ya yi aikin sanin makamar aiki a Jami’ar Jihar Ebonyi, daga baya ya koma Amurka da aiki.
- Yanzu haka malamin aikin likitanci ne sannan darakta ne a Shirin Gwajin Magunguna Cutar AIDS a Tsangayar Koyar da Aikin Likitanci ta Jami’ar Yale ta kasar Amurka.
- Shi ne ya jagoranci Bincike da Gwaje-gwajen Magungunan COVID-19: remdesivir (wanda Hukuma Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da shi); leronlimab da remdesivir; hadin tocilizumab da kuma gwajin rigakafin da Pfizer/BioNTech suka samar.
- Dokta Onyema Ogbuagu ‘yan biyu ne kuma dan uwansa da ka haife su tare Injiniya ne.