Tayar da kura ba bakon abu ba ne a fagen wasanni a Najeriya, duk da cewa ana samun nasarori da dama wajen bunkasa bangaren.
An shiga wannan shekarar ta 2021 ce da radadin ficewa daga kullen annobar coronavirus da ta dakatar da harkokin wasanni a bara kafin aka dawo daga bisani.
- Allah Ya yi wa Shugaban Gidauniyar A.A Rano rasuwa
- Basaraken Filato ya kubuta daga hannun ’yan bindiga
Wannan ya sa Aminiya ta rairayo wasu muhimman abubuwan da suka faru a fagen wasanni da za a dade ba a manta su ba.
Zanga-zangar ’yan wasan Olympic na Najeriya a Tokyo
’Yan wasan Najeriya sun tafi birnin Tokyo da ke kasar Japan ne da zummar dawowa da kambunan nasarori da dama, amma a ana tsaka da wasannin gasar, sai ’yan wasan Najeriya da masu horarwa da shugabanninsu suka shiga rikice-rikice da har ya kai ga zanga-zangar wasu daga cikin ’yan wasan, wanda ya jawo wa kasar abin kunya a idon duniya.
Farkon abin kunyar da aka samu shi ne yadda Hukumar Kwastam ta kama kayan ’yan wasan da kamfanin Peak ta hada wa ’yan wasan bayan sun shiga yarjejeniyar daukar nauyin kayan ’yan wasa da Hukumar Kwalon Raga ta Najeriya na shekara hudu.
Ana cikin haka ne kuma bayan wasanni sun nisa, sai Kwamitin Shirya Wasannin ya dakatar da ’yan wasan tseren Najeriya guda 10 bayan sun fadi gwajin da kwamitin ta gindaya domin shiga gasar.
’Yan wasan da aka dakatar su ne Knowledge Omovah da Ruth Usoro da Favor Ofili da Rosemary Chukuma da Glory Patrick da Yinka Ajayi da Tima Godbless da Chidi Okezie da Chimaoma Onyekwere da Annette Echikunwoke.
Kafin fara gasar, kamfanin Samsung ya yi alkawarin ba kowane dan wasa wayar Samsung samfurin S20+ 5G. ’Yan wasan da aka dakatar ne suka samu labarin Kwamitin Gasar na Najeriya ya karbi wayoyin a madadinsu, wanda hakan ya sa suka gudanar da zanga-zangar rashim amincewa, inda suka zargi kwamitin da laifin da ya sa aka dakatarsu daga fafatawa a gasar.
Daga baya an ba su wayoyinsu bayan duniya ta dauka.
Ana cikin ce-ce-ku-cen zanga-zangar ce kuma aka wayi gari da bidiyon daya daga cikin ’yan wasan Najeriya Chukwuebuka Enekwechi a Instagram yana wanke rigar wasansa ta Najeriya.
Zanga-zangar ’yan wasan kwallon raga saboda rashim biysan su alawus-alawus
Bayan nasarar da tawagar kwallon ragar Najeriya, D’Tigers ta samu a gasar Afrobasket Championship, an tsinci bidiyon ’yan wasan a kafofin sadarwa suna zanga-zanga kan rashin biyan su kudaden alawus dinsu, inda suka zargi Hukumar Kwallon Raga da Ma’aikatar Wasanni da danne musu kudaden, sannan suka yi barazanar cewa ba za su amsa kiran buga wasannin neman gurbin shiga gasar ta duniya ta shekarar 2022 ba matukar ba a biya su hakkokinsu ba.
Sai dai tuni aka biya su kudaden bayan sun nuna fushinsu.
Kunyata ’yan wasan Najeriya mata a Legas
A wannan shekarar ce kuma kungiyar wasan kwallo ta mata da Afirka ta Kudu, Bayana Bayana ta doke kungiyar wasan kwallo kafa mata ta Najeriya Super Eagles da ci 4 da 2 a wasan karshe na gasar cin Kofin Aisha Buhari da aka buga a Jihar Legas ta Najeriya.
Wasan ya matukar ba mutane mamaki ganin ’yan wasan Najeriya sun dade suna cin karensu babu babbaka a Afirka, amma a zo har gidansu a doke su a Gasar Cin Kofin Uwargidan Shugaba kasarsu.
Tawagar Jamhuriyar Central Afirka ta doke Super Eagles a Najeriya
A karon farko a tarihi wasannin kasar Central African Republic, (CAR), ’yan wasanta sun zo har gida sun doke Super Eagles ta Najeriya da ci daya da nema a Legas.
Wannan wasa ya matukar jawo wa kasar dariya, sannan da yawa daga cikin ’yan wasan suka ki halartar wasanni biyu na sada zumunci da Kamaru bayan wannan,
Daga bisani kuma aka samu labarin cewa sun ki zuwa ne saboda bashin kudaden da suke bi, lamarin da ya jawo musu nuna yatsa daga wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka bayyana su a matsayin marasa kishi.
Sallamar Kocin Super Eagles, Gernot Rohr
Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (NFF) ta sanar da ta raba-gari da tsohon kocin Super Eagles din, Gernot Rohr, bayan ya kwashe kimanin shekara biyar yana horar da ’yan wasanta.
Sallamar Gernot Rohr ta haifar da muhawara mai zafi a fagen wasanni, inda wasu ke kuka wasu kuma na dariya.
Daga cikin masu farin cikin sallamar kocin, akwai masu ganin ba ya son amfani da ’yan wasan da suke taka leda a Gasar Firimiyar Najeriya, da kuma rashin tabbataccen tsarin wasanni.
Gayyatar ’yan wasan Firimiyar Najeriya zuwa gasar Kofin Afirka
Bayan an sallami Gernot Rohr, sai Hukumar NFF ta nada Austin Eguavoen a matsayin kocin Super Eagles na wucin-gadi har zuwa kammala Gasar Kofin Afirka wanda za a fara a watan Janairu 2022 a kasar Kamaru.
Babban abin da ya yi da ya sanya murna a zukatan masoya kasar, musamman masu bibiyar Firimiyar Najeriya shi ne sanya ’yan wasan da ake ganin ba kowa ba ne domin wakiltar kasar, wanda yana cikin abin da aka rika zargin tsohon kocin da rashin kokarin yi.
Masu sharhi a kan wasannin Najeriya suna ganin samun ’yan wasan gasar suna buga wa Super Eagles zai taimaka wajen karkafa gwiwar masu buga gasar, kuma zai kara gyara gasar.
’Yan wasan biyun da aka dauka su ne John Noble, wanda gola ne na kungiyar Enyimba FC ta Jihar Abia, sai Olisa Ndah, wanda da shi aka lashe Gasar Firimiyar Najeriya ta kakar bara a kungiyar Akwa United, duk da cewa yanzu ya koma kungiyar Orlando Pirates ta kasar Afirka ta Kudu. Sai kuma Daniel Akpeyi wanda shi ma yake kungiyar Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu.
Super Eagles ta yi sabon koci
Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (NFF), ta sanar da daukar Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.
Hukumar ta sanar da hakan bayan taronta na ranar Laraba.
Jose Santos Peseiro tsohon dan kwallo ne mai shekara 61 da ya buga tamaula a matsayin dan wasan gaba.
Daga cikin kungiyoyin da ya horar akwai Real Madrid a matsayin mataimakin koci, da FC Porto da Sporting CP, sai kasashen Saudiyya da Venezuela da sauransu