A ranar Asabar Allah Ya karbi ran tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Ogun ta Gabas, Sanata Buruji Kashamu bayan ya yi fama da cutar COVID-19.
Abokin marigayin kana tsohon dan Majalisar daga Jihar Bayelsa, Sanata Murray Bruce ne ya sanar da mutuwar a shafinsa na sada zumunta.
Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Sanata Buruji Kashamu da Aminiya ta kawo muku:
- An haifi Sanata Buruji Kashamu a Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya a Shekarar 1958.
- Ya fara karatun firamare a makarantar Ansaru da ke garin Ijebu Igbo a Jihar sannan ya koma makarantar St. John a Legas wadda ya gama a shekarar 1972.
- Ya ci gaba da karatu a ajujuwa na musamman da yammaci a Kwalejin Igobi, inda ya hada aiki da karatun.
- Daga nan ya tafi kasar Ingila ya yi kwasakwasai a fannin kasuwanci a Kwalejin Pitman da ke birnin London.
- Jami’ar Diploma-mill Cambridge da ke Massachusetts, wacce ba a tantance ta ba, ta ba shi shaidar digirin digirgir, a wani biki da aka yi a sirrance a Legas.
- Mamacin daya ne daga cikin jigajigan jam’iyar adawa ta PDP a jihar Ogun, kana shi ne dan takarar gwamnan jihar na jam’iyar a zaben shekarar 2019.
- An taba korar sa daga jam’ iyar ta PDP a shekarar 2018 amma wata Babbar Kotu a Abuja ta soke korar a watan Oktoban 2018.
- A shekarar 1998 an kama shi a kasar Birtaniya bisa zargin badakalar safarar miyagun kwayoyi bayan da aka same shi da kokarin shiga kasar da Dalar Amurka 230,000.
- A sheakar 2003 aka sake shi, bayan wata kotu ta wanke shi.