A wannan makon Gizago ya waiwayi al’amarin marigayi Mu’ammar Gaddafi, tsohon Shugaban Kasar Libya, wanda aka kashe shekaru 11 da suka gabata.
Shin tun bayan mutuwar tasa, ko al’ummar kasar Libya sun samu madadinsa? Ku taya mu dubawa.
- Kofin Duniya: Salsala da sauye-sauyensa a tarihi
- ’Yan bindiga da ’yan daba suna ci gaba da addabar Amurka da Ingila
A ranar 20 ga Oktoban 2011 ce al’ummar duniya suka gamu da mummunan labarin kisan gilla, kisan wulakancin da aka yi wa shugaban-shugabannin Afirika, jan gwarzo Mu’ammar Gaddafi.
Babu shakka duk wani mai bibiyar al’amuran da ke gudana a duniya ya dade da sanin jarumtaka da gwarzontakar Shugaba Gaddafi, musamman ma yadda ya tsaya kai da fata, cikin kishin kasa da kishin al’ummarsa.
Yadda ya shugabanci kasarsa ta Libya cikin adalci da kishin al’umma.
Haka kuma, shaida ta tabbatar da yadda ya kasance mai kare muradun raunanan kasashen Afirika da yadda ya yi ta gwagwarmaya da azzaluman kasashen waje.
Wannan dalili ne ma ya sa suka kafa masa kahon zuka, har suka yi sanadiyyar halaka shi.
A lokacin da muke jimamin tuna wannan jan gwarzo, bari mu dan bincika wasu ayyukan alheri da ya gudanar a rayuwarsa, a matsayinsa na shugaba mai kishin addinin Islama, mai kisihin al’ummarsa. Shugaban da ba ya jin tsoron Yahudu da Nasara.
A lokacin da Gwarzo Gaddafi ke mulki a kasar Libya, ya kyautata wa al’ummarsa, musamman ma matasa da ke son aure, yana ba ango da amarya Dalar Amurka dubu hamsin, domin su kawata gidan da za su zauna domin cin amarci.
Ilimi kuwa tun daga firamare har zuwa jami’a, kyauta ake ba duk wani dan Libya. Wannan ta sanya harkar ilimi a kasar ta bunkasa, domin kuwa kafin ya samu kansa a karagar mulki, kashi 25 cikin dari na al’ummar Libya ba su da ilimi, amma bayan ya hau mulki sai al’amuran ilimi suka bunkasa, ta yadda kashi 83 cikin dari na daukacin al’ummar kasar suka zama masu ilimi.
Ga duk wani dan Libya da ya zabi ya yi noma, za a ba shi isasshen filin noma kyauta, a ba shi gidan gona, a ba shi dabbobin da zai yi kiwo da kuma na’u’ororin noma na zamani.
Duk kyauta za a ba mutum wannan, ba don komai ba sai don sana’arsa ta inganta kuma ya bunkasa kasarsa da abinci.
Ta fannin kiwon lafiya kuwa, al’ummar Libya ba su biyan kokwabo a asibitocin kasar. Magani da duk wani abu da likita zai yi wa mutum, duk kyauta ne.
Ba wannan ba ma, a lokacin da dan Libya ya kamu da wata rashin lafiya, aka ga cewa sai an kai shi kasashen waje don neman magani, gwamnati ce za ta biya duka dawainiyar maganin, sannan za a rika ba majinyacin dalar Amurka 2,300 kowane wata don biyan wasu hidindinmu har ya warke ya dawo gida.
Ta fuskar harkokin sufuri kuwa, al’amuran hanyoyi duk ya inganta su, sannan kuma idan dan kasa yana son sayen mota, gwamnati za ta biya masa kashi 50 cikin dari na jimillar kudin motar.
Man fetur kuwa, a Libya ana sayar da shi a kan kimanin darajar Naira 22 lita daya.
Wannan kuwa ba komai ba ne ga mutumin Libya, saboda kudinsu suna da matukar daraja da albarka.
Kasar Libya a karkashin marigayi Gaddafi ba ta cin bashi ba. Babu kasar da ke bin ta bashin ko kwabo.
Haka kuma, tana da makudan kudi, kimanin Dala bilyan 150 a asusunta na ajiya da ke kasashen waje.
A Libya, wutar lantarki kyauta ce, babu wani magidanci da ke biyan kudin wuta. Bankuna a kasar kuwa ba su ba da bashi da ruwa.
Duk wanda aka ranta wa kudi, ba zai biya ko sisin kwabo ba a matsayin ruwa, abin da aka ranta masa, shi zai biya daidai.
Ruwan sha kuwa ko na noman rani, gwamnatin Libya ta wadata shi ga al’umma. Babu wahalar ruwa, duk kuwa da cewa kasarsu sahara ce.
Amma ya jawo ruwa tun daga Kogin Nilu, wanda ya wadata kasar da albarkatun ruwa.
Idan dalibi ya kammala karatu a Libya kuma bai samu aiki ba, gwamnati za ta rika biyan sa albashi duk wata, daidai da satifiket dinsa har sai ya samu aiki ko sana’a.
Idan kuwa mace ta zo haihuwa a Libya, gwamnati za ta ba ta Dala dubu biyar a matsayin tukwici.
Kafin ya rasu, Shugaba Mu’ammar Gaddafi ya bar wata rubutacciyar wasiyya, wacce kuma ke kara nuna daukakarsa da muhibbarsa kuma ke kara tabbatar da cewa shi ingantaccen Musulmi ne mai kishin addininsa.
Ga abin da wasiyyar tasa ta kunsa: “Wannan ita ce wasiyyata. Ni Mu’ammar bin Muhammad Abdussalam bin Humayd bin Abu Manyar bin Humayd bin Nayil al Fuhsi Gaddafi, na rantse babu wani abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzon Allah ne (SAW).
“Na dauki alkawarin zan mutu ina matsayin Musulmi. Idan an kashe ni, ina son a rufe ni bisa ka’idar Shari’ar Musulunci, kuma a rufe ni da suturar da nake sanye da ita kuma kada a yi mini wanka.
“Ina son a rufe ni a makabartar birnin Sirte, kusa da iyalina da ’yan uwana. Ina son a kyautata wa iyalina bayan na mutu, musamman matata da yara.
“Ina son al’ummar Libya su kare mutuncin kansu da alfaharin kasarsu da tarihinsu da kuma kare mutuncin magabatansu, wato shugabanninsu da jarumansu.
“Ina kada son al’ummar Libya su gaza wajen sadaukar da kansu domin ’yanta kasarsu, kamar yadda magabatansu suka kasance ’yantattu masu ’yanci.
“Ga magoya bayana kuwa, ina kiran da su ci gaba da tirjiya da gumurzu da azzaluman kasashen duniya da suke zaluntar kasarmu ta Libya. Su ci gaba da wannan yaki a yau da gobe da kowane lokaci.
“Bari in sanar da al’ummar duniya masu ’yanci cewa, da mun so da sai mu yi yarjejeniya da azzalumai, mu sarayar da ’yanci da dukiyar kasarmu, domin mu ji dadin rayuwarmu ta kashin kanmu.
“Kuma ina sanar da su cewa, an yi mana tayi da dama don mu yi haka, amma sai muka zabi mu ci gaba da gwagwarmaya domin mu kasance masu ’yanci da mutunci.
“Kuma ya kamata mu sani, ko da ba mu ci nasarar wannan gwagwarmaya ba a yanzu, za mu bar darasi da misali ga al’ummarmu da ke tafe nan gaba, domin su gane cewa kare mutuncin kasarsu shi ne abin alfahari, a yayin da sayar da mutuncinta kuwa ya kasance babban cin amana, wanda tarihi zai tabbata yana tunawa da shi.”
A yayin da Gwarzo Gaddafi ya amsa kiran Allah (SWT), addu’armu a kullum ita ce, Allah Ya jikansa, Allah Ya kyautata makwancinsa.
Azzaluman da suka yi sanadiyyar kashe shi kuwa, muna rokon Allah Ya cika alkawarinSa a kansu. Mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani. Amin-summa-amin!