Wani mutum ne yana cikin otel, sai ya duba dakin da ya sauka, sai ya ga akwai kwamfuta. Saboda haka sai ya hau domin ya mika sako ga matarsa ta Imel.
To ashe ya yi kuskuren shigar da sakon zuwa ga wani adireshin, wanda ba na matarsa ba, na wata matar ce daban, wacce mijinta ya mutu a daidai lokacin, domin a lokacin ba a fi awa biyu da kai shi makwancinsa ba.
To sai matar nan ta hau kwamfuta don ganin sakonnin ta’aziyyar da aka aiko mata.
Tana gama karanta sako na farko sai masu amsar gaisuwa da ke tare da ita suka ga ta fadi a sume.
Suna duba fuskar kwamfuta, sai suka ga sako kamar haka: “Zuwa ga matata. Na san za ki yi mamakin ganin wannan sakon nawa.
“To, ba abin mamaki ba ne, domin gaskiya wurin yana da kyau saboda akwai duk wani abin more rayuwa, har da kwamfuta da kayan alatu.
“Saboda haka, ke ma na gama shirya miki komai, saboda gobe za ki biyo ni, mu ci gaba da zama tare…”
Su ma masu ta’aziyya suna gama karantawa sai gudu.