✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Direba da dan sanda

To wa ya ce ka rika tafiya kai daya a mota, idan wani abu ya same ka wa zai mai da ka gida.

Wani dan sanda ne ya tsare direba inda ya fara yi masa tambayoyi kamar dai yadda jami’ai suka saba yi wa masu ababen hawa a kan hanya.

Ga yadda tattaunawarsu ta kasance:

Dan sanda: “Ina takardun motarka?”

Direba: “Ga su nan.”

Dan sanda: “Ina lasisinka?”

Direba: “Ga shi nan.” (Komai aka tambayi direba yana da shi, dan sanda ya gaza kama shi da laifi).

Dan sanda: “To wa ya ce ka rika tafiya kai daya a mota, idan wani abu ya same ka wa zai mai da ka gida?”

Direba: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu wata addu’a, a duk lokacin da zan yi tafiya, idan na karanta ta, mala’iku dubu suna tare da ni.”

Dan sanda: “Mala’iku dubu a karamar mota? To ka yi obalodi, mu tafi ofis, na kama ka!”

Daga Isma’il Lawal Gambo