✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Ban gan su ba!

Kudi ne ka zubar cikin bakar leda nan wurin ’yan Naira dubu guda uku ko.

Wani Bakatsine mai suna Buba ya zubar da kudi sai ya zo yana ’yan dube-dube, amma bai dai yi cigiya ba.

A wurin akwai wani Bahadeje mai suna Ilu, sai ya kada baki ya ce wa Buba: “Kudi ne ka zubar cikin bakar leda nan wurin ’yan Naira dubu guda uku ko.

“Kuma an daure su da tsumma. Sababbi ko?”

Sai Buba ya ce: “Eh, su ne kuwa!” Sai Ilu ya ce: “Ban gan su ba!”

Daga Amiru Isah Bakori