Wani farfesa ne ya fita yawon shakatawa. Bayan tafiya ta yi tafiya sai ya isa wani kauye mai babban kogi.
Farfesan ya ga jama’a na shiga jirgin ruwa don hayewa.
Bayan sun yi nisa da tafiya sai mai jirgin ya bukaci kowa ya kawo kudin jirginsa.
Bayan an bayar sai farfesa ya ce, “A ba ni rasiti?”
Mai jirgi ya ce, “Ni ban san rasiti ba.”
Farfesa ya ce, “Ko takarda ka rubuta ka ba ni.”
Mai jirgi ya ce shi bai iya rubutu da karatu ba.
Sai farfesa ya ce, “Amma ka yi asarar zuwa duniya.
Bayan sun kusa gaba sai igiyar ruwa ta nemi kada jirgi, mai jirgi ya ce wa fasinjoji, “Kowa tasa ta fisshe shi, na yi bakin kokarina, amma abin ya fi karfina.”
Jama’a suka yi ta fadawa ruwa suna hayewa.
Sai farfesa ya ce wa mai jirgi, “Ai ni ban iya ruwa ba.”
Mai jirgi ya kada baki ya ce masa: “Tun da ba ka iya ruwa ba, amma ka yi asarar zuwa duniya.”
Daga Kwamared Yusuf Lawal Amaru Zariya