Saurayi da surukinsa
Wani saurayi ne yana son wata yarinya, ran nan sai ya shirya zai je su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ya isa gidan surukan nasa yana shan taba. Ga yadda hirarsu ta kwashe da mahafin yarinyar:
Saurayi: Baba ina kwana?
Baba: Lafiya lau, ashe dama kana shan taba?
Saurayi: A’a, ba halina ba ne, na saba ne idan na sha giya ba na jin dadi, sai na sha taba.
Baba: Tabdi! Wato har giya ma kake sha ke nan?
Saurayi: A’a, idan na je gidan rawa ne kawai nake sha.
Baba: To, har gidan rawa kake zuwa?
Saurayi: Eh! Amma da can ba na zuwa, sai da na dawo daga gidan yari ne na fara zuwa.
Baba: Gidan yari fa ka ce, kai kuma me ya kai ka can?
Saurayi: Kaddara ce ta sa na je, kisan kai na yi.
Baba: Kisan kai, wa ka kashe?
Saurayi: Wani baban budurwata na kashe saboda na tambayi auren ’yarsa ya hana ni.
Baba: Kai, Lale marhabin da saurayin ’yata. Gobe ka turo iyayenka mu yi maganar aure. (Mahaifin ya yi haka ne saboda tsoro, ya ji zancen kisa).
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382.
Bahadeje mai Turanci
Wani Bahadeje ne daga Jihar Jigawa ya je wajen intabiyu, don a dauke shi aiki kuma an sanar da shi cewa da Turanci ake gudanar da ita. Shi kuma ya dauka komai aka tambaye shi da Turanci zai amsa. Ga yadda intabiyun ta kasance:
Malami: What is your name? (Yaya sunanka)?
Bahadeje: New 10 Kobo (Sabo Sule).
Malami: From which LGA? (Daga wace Karamar Hukuma)?
Bahadeje: From Stone LGA (Dutse LGA).
Malami: What is the work of your father? (Me ke sana’ar babanka)?
Bahadeje: Lorry Dog (Karen Mota).
Malami: Which kind of lorry? (Wace irin mota yake tukawa)?
Bahadeje: Dismiss the Hyena (A-Kori-Kura).
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011
Ni barawon babur ne!
Wani ne matarsa ta haifi jaririn da bai zo da rai ba a asibiti. Sai ya samu babban kwalin biskit ya saka gawar jaririn a ciki, ya dora a kan babur. Ya bar babur din a kafe, ya je cikin asibiti domin ya sallami likita. Koda ya dawo sai ya samu an sace babur da gawar da ke cikin kwalin. Barawon yana tafiya sai ya hadu da ’yan sanda, ya ciro Naira dari ya ba su, ya ce: “Oga ina sauri ne!” Wani dan sanda ya ce: “To ka ba mu biskit din mana.” Barawo ya bude kwalin da nufin ciro biskit, sai ga gawar jariri kwance. Sai barawo ya ce: “Wallahi oga ni ba barawon yara ba ne, ni barawon babur ne!”
Daga Sunusi NNPC, 08034367040
Da ban taso ba da ni ta dauka!
Wani Bafulatani ne ba ya da lafiya, aka kwantar da shi a asibiti yana jinya. Sai ya ga majinyaci na gadon farko ya rasu, na biyu ma ya rasu sai aka tsallake shi, wancan ma na kusa da shi ya rasu; saura shi kadai a layin. Yana ganin haka sai ya tashi ya ce: “Wallahi mutuwar manta ni ta yi, ba zan zauna ba, domin dawowa za ta yi ta kaina. Nan take ya sallami kansa daga asibitin. Likita ya gamu da shi ya ce masa: “Ai ba ka warke ba, ka ga wuyanka ko juyawa ba ya yi.” Ya ce: “Eh, na tafi.” Ya ce wa matarsa: “Ko ki debo kayan ki taho, ko ki zauna, ni na tafi.” Suna tafiya a ranar aka kawo wani a gadon da ya tashi. Mutumin ko awa uku bai yi ba shi ma ya ce ga garinku nan. Da Bafulatanin ya samu labarin sai ya ce: “Tab, ai ku duk ba ku da hankali, da ban taso ba, da ni ta dauka.”
Daga Sunusi Ubankulob Garko, 07038766018