✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Za a yi sanyi Wani Bahadeje ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan…

Za a yi sanyi

Wani Bahadeje ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida, ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi. Ki shiga ki gyara masa dakin baki da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki, tana gamawa sai suka fito ba su ga Bahadeje ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, ya jike jagaf. Sai baban ya tambaye shi cewa: “Daga ina haka?” Sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”

Daga Nura Suleja, 09027377656

 

Tasu kawai nake sha!

Wani mutum ne kullum ya je gidan giya sai ya sha kwalba uku, wata rana sai mai gidan giyar yake tambayarsa: “Wai me ya sa kowa yana shan daya amma kai kake shan uku?” Sai ya ce ai sun yi alkawari shi da abokansa biyu, daya yana kasar Indiya, dayan kuma a kasar Rasha, duk wanda zai sha giya sai ya sha wa ’yan uwansa. A kwana a tashi, ran nan sai ya zo ya sha kwalba biyu, sai mai gidan giyan ya tambaye shi cewa a cikin abokan nasa wanne ne ya mutu? Sai ya ce: “Ba kowa, ni ne dai Allah Ya shirye ni, tasu kawai nake sha.”

 

Kadan-kadan

Wata rana ne aka hada baki da mai sayar da shayi aka ba wani kurma shayi mai zafi. Da ya yi kurbar farko, sai ya watsar, cikin dimautar zafi sai ya ce: “A fafi (da zafi).” Mutanen da ke wurin wadanda kuma da su aka shirya wa kurman nan shakiyanci, suka kama baki don mamaki, suka kalle shi baki bude, suka tambaye shi cewa: “Ashe da ma kana magana?” A take sai kurman ya zaro idanu yana kallonsu, ya ba su amsa da cewa: “Kadan-kadan!”

Labarai daga Nasiru Kainuwa Hadeja, 08100229688

 

Tsuntsuwar gida

Wani yaro ne da mahaifiyarsa suke tattaunawa, kamar haka:

Yaro: Mama ina da tambaya. Mama: Mece ce tambayarka? Yaro: Wai Ladi ’yar aikin gidan nan tana da fiffike? Mama: (dariya), me ka gani? Yaro: Jiya da baki nan sai na ji Baba yana ce mata “Ladi tsuntsuwar zuciyata.” Yana ta zuga ta, ita kuma tana dariya. Mama: Kwarai da gaske tana da fiffike, domin yau-yau din nan za ta tashi ta koma kauyensu.

 

Ashe kun gane!

Wani mutum ne ya sayo sabuwar mota kirar Jeep, an rubuta 4d4 a jikinta. Sai wani malamin makaranta mai tabin hankali ya zo wucewa ya gani, sai ya ce: “Kai wadannan wadanne irin tsofaffin dakikai ne, har yanzu ba su gane amsar nan ba?” Sai ya dauko kusa ya rubuta 16 a jikin motar. Da mai mota ya gani sai ya yi ta fada, ya je ya sa aka goge, aka gyara wurin. Wata rana mahaukacin ya dawo ya ga an gyara, sai ya sa kusa ya sake rubuta 16. Mai mota ya ga haka sai ya canja shawara, ya je wurin masu zane aka rubuta 16 da kyawun rubutu don kada a sake bata masa mota. Sai mahaukacin ya dawo ya ga an rubuta amsa daidai sai ya dauko kusa ya ce: “Ya ce ashe sun gane.” Sai kawai ya rubuta Bery Good a jikin motar.

Labarai daga Mudassir Mai Shayi Ningi, 09025297045