✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu san shugabanninmu2

Barka da warhaka Manyan Gobe Yaya karatu? Ina fata kuna  cikin koshin lafiya. A wannan makon Kawunku Ibrahim IBB Kazaure ya yi muku guzurin tarihin…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Yaya karatu? Ina fata kuna  cikin koshin lafiya.
A wannan makon Kawunku Ibrahim IBB Kazaure ya yi muku guzurin tarihin tsohon Shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abaca don ku san tsofaffin shugabanni. Ina fata za ku bi rubutun sau-da-kafa.
A sha karatu lafiya:
Naku Kawu Bashir Musa Liman

Mu san shugabanninmu

Daga Ibrahim IBB Kazaure

An haifi Janar Sani Abaca ranar 20 ga watan Satumba, 1943 a  cikin garin Kano.  Ya yi makarantar Firamare a City Senior Primary School,  Kano, sai Gobernment College Kano, daga 1957 zuwa1962, sai Kwalejin Horar da Sojoji ta  Kaduna daga 1962 zuwa 1963. A shekarar 1963 ya je Kwalejin Horar da Sojoji ta Aldershot da ke Ingila, daga nan sai Kwalejin Horar da Dakarun kasa ta Warwick da ke Birtaniya a 1966.
Daga nan a 1971 ya koma Kwalejin Sojoji ta Jaji da ke Kaduna Najeriya. A 1976  ya shiga Kwalejin Nazarin Manufofi da Tsara Dabarun Mulki da ke Kuru, a Jihar Filato. A 1981 da 1982 ya yi wasu kwasa-kwasai da suka shafi harkar tsaro a Kanada da kuma Amurka.
 Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 Abaca ke taka rawar gani a wannan kasa wadda ta kai tarihi ba zai taba mantawa da shi ba.
A karkashin mulkinsa ne PTF ta karade Najeriya da aiki har yanzu akwai aiyukan PTF a garuruwanmu. Bayan ayyuka masu tarin yawa wanda ya gudanar a karkashin mulkinsa.
Abaca ba ya son wargi, ko tashin hankali ya samar da tsaro a lokacinsa.
Allah Ya yi masa rasuwa ranar 8 ga watan Yuni, 1998 yana da shekaru 54 sakamakon ciwon zuciya. Ya bar mata daya Hajiya Maryam Abacha da ‘ya ‘ya tara, mata uku; maza shida.