✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu sake duba tasirin taimako a rayuwa

A yau kuma za mu duba muhimmanci, tasiri da kuma dinbin sinadaran da ke tattare da taimako ga rayuwarmu ta yau da kullum, a matsayinmu…

A yau kuma za mu duba muhimmanci, tasiri da kuma dinbin sinadaran da ke tattare da taimako ga rayuwarmu ta yau da kullum, a matsayinmu na mutane. Abu ne da ya kamata kowa ya gane cewa, duk wani dan Adam, komai mukaminsa, komai karfin arzikinsa, komai karfin jikinsa, yana bukatar taimako. Idan ba ya bukatar tallafin dukiya, to yana bukatar wani, idan bai bukatar wani tallafin, to ala tilas dinsa, yana da wata bukatar daga dan uwansa mutum.
Kamar yadda al’amarin yake, Allah Ya halicci dan Adam ne a matsayin mai kasawa, wanda dole ne ya zama yana dogara da dan uwansa. Ke nan, babu yadda za a yi mutum ya rayu shi kadai ta karan kansa. Yana bukatar rayuwa cikin kininsa mutane, ba dabbobi ba. Koda mutum ya yi kankanbar kaurace wa jama’a, ya ce zai rayu a matsayinsa na tilon mutum, to babu shakka ba zai samu dacewa da ingantattar rayuwa ba. Babu shakka zai gamu da cikas a fannoni da dama da zai fuskanta.
Idan mun kasa tsintar fa’ida daga wannan bayanin da ya gabata, bari in yi mana gwari-gwari, inji matar bagwari. dan Adam, a matsayinsa na mai kasawa, yakan zo duniya ne a matsayin dan labubu, wanda ke bukatar dukkan wani taimako. A wannan lokacin, sai an taimaka masa sannan yake samun iskar shaka, wacce ke taimaka masa don ya rayu. Sai an taimaka masa sannan zai samu dan abin da zai ci. Hatta bakinsa da zai sha abin da zai sha, bai san amfaninsa ba, sai an taimaka masa, an sanar da shi.
Ban da wannan, a kan taimaka wa dan Adam da sutura, domin kuwa bai zuwa da komai a jikinsa, yakan zo a matsayin tuburarre, kuma hannusa babu komai, watau fankan-fayau yake zuwa. Amma ko da iyayensa sun fi beran masallaci talauci, sai sun taimaka masa da suturar da za ta suturce masa tsiraicinsa.
A wannan lokacin, bai ma san inda ke masa ciwo ba balle ya nemi magani. Iyayen nasa ne za su yi amfani da hikima, su gano dalilin da ya sanya yake kyakyata kuka, sannan kuma su gano tare da binciko magani ko kuma mutumin da zai ba shi magani. Bayan sun samo maganin, su za su taimaka su ga cewa ya sha maganin kuma ya yi masa aiki. Wannan duk taimako ne ake yi masa, wanda idan ba a yi ba, kila daga nan azabar ciwon ta gallabe shi, wanda mai yiwuwa idan bai da sauran kwana gaba, sai ya koma inda ya fito.
Haka dai za a ci gaba, har yaro ya ci gaba da girma, sannan a ci gaba da ba shi abinci da abin sha da sutura. Sannan kuma a yi ta taimaka masa da hudubobi da shawarwari, sannan ma har a sanya shi makaranta, duk dai domin ya samu cikakken hankali da halayen kwarai, ta yadda zai zama mai dogaro da kansa. Wannan duk wasu nau’ukan taimako ne da ake masa, wadanda idan ba a yi masa su ba, babu yadda za a yi ya samu sa’idar rayuwa cikin dadi.
Idan kuma ya girma, ba shi ke da dubarar samun aiki ko sana’ar da ya samu ba. Sai da ya shiga hannun wani ko wata, sannan ya koya, ya iya. Sai da aka tallafa masa, aka taimaka masa, aka dauke shi aiki, ko kuma aka taimaka masa da jari, sannan ya samu duk wani abu da ya samu a ma’aikatar ko kuma a wurin sana’ar tasa. Ashe lallai mutum ya samu tallafi da taimakon wasu, kafin ya samu nasara a rayuwa.
Ina fatan yanzu dai duk an gane misalaina, kuma an ankara da dalilan da ke nuna cewa mutum, ko shi wane ne, yana bukatar taimako. Babu shakka na san yanzu an gane da haka. Idan mutum na ganin yanzu ya zama attajiri, to lallai yana bukatar taimako ta bangarori da dama. Dole sai an tallafa masa kafin ya samu damar watayawa, domin kuwa akwai abubuwa da yawa da ba zai iya aiwatarwa ba da kansa. Ko da biya zai yi a yi masa da kudi, taimako ne dai, domin wani dan Adam din ne zai aikata masa.
A lokacin da muka kasance attajirai, muna jin cewa lallai dukiya ba matsala ba ce a rayuwarmu. To, mu waiwaya baya mu taimaki wadanda ba su da shi, domin mu ma an taimaka mana a lokacin da ba mu da shi. kwarai kuwa, domin kuwa idan mun tuna, mu ma an taimaka mana a lokacin da muka zo duniya a matsayin tsirara, ba tare da komai ba a hannunmu ko a jikinmu. Idan mulki ne Allah Ya ba ka, lallai akwai bukatar ka yi amfani da wannan mulki domin taimakon dan uwanka mutum mai rauni, domin kai ma an taimaka maka kuma akwai ranar da za ka dawo kan dole ka nemi taimakon mutane. Idan ilimi ne Allah Ya wadata ka da shi, sai ka yi himma ka taimaka wa jahilai domin su samu wannan ilimi, domin akwai lokacin da kai ma ba ka da shi, sai da wani ya taimaka maka. Domin a lokacin da kake jahili, wani kuwa yana da dinbin ilimi, sai ya taimaka maka ya koya maka wani bangare na iliminsa, wanda dalili ke nan ya sanya ka zama malami a yanzu. Ke nan, kwaryar da ta je, kamata ya yi ta dawo.