✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu nazarci wasu sinadaran kyautata rayuwa (3)

Ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa; Assalamu alaikum. Bayan haka, yau mako uku ke nan da muka faro yin nazari da tambihi kan wasu abubuwa hurhudu da…

Ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa; Assalamu alaikum. Bayan haka, yau mako uku ke nan da muka faro yin nazari da tambihi kan wasu abubuwa hurhudu da muka ce sinadaran kyautata rayuwa ne. Wannan makon ma za mu ci gaba.
Ba tare jinkiri ba, yanzu za mu dauki tubali daya cikin hudun nan, domin mu soma gina bayaninmu na yau. Wannan sinadari ko tubali shi ne karya. Abin da ya sanya muka dauke ta a matsayin tubali abin kulawa a yau shi ne, kasancewarta wani babban jigo da ke ruguza al’amuran kwarai. Duk inda ake maganar mutunci da kamala, idan aka kawo batun karya, za ka samu cewa ba ta da wani tasiri a cikin al’amari. Za ka ji ana kushe ta, ana yi Allah-wadai da ita da kuma mai yin ta, saboda muninta da kuma rashin dacewarta da hanyar kwarai.
Wani mai basira ya yi wa karya kirari, inda yake cewa: “karya linzamin Shaidan, mai sarrafa ki sai dan bogi…!” karya, mummunar abu ce da ke zubar da kwarjini da martabar mutum. Duk lokacin da mutum ya fadi karya, to ya shuka wani mugun iri ne a cikin martaba da mutuncinsa, wanda duk ranar da tsironta ya fito, ya yi rassa, ya yi fure kuma ya yi ’ya’ya, to a lokacin ne mutum zai gane kurensa. karya, komai dadewar lokacin faruwar ta, sai ta tonu, domin kuwa komai dadewa da jinkiri sai kishiyarta, gaskiya ta fito. Duk lokacin da gaskiya ta bayyana kuwa, to karya ai sai ta koma makwafinta.
Shawararmu a nan ita ce, duk yadda ka kai ga son boye wani al’amari, kada ka sake ka fadi karya. Ya fi kyau ka fito fili ka fadi gaskiya kuma ka zama mai gaskiya. Koda an ki ka don gaskiyarka da fadin gaskiyarka, babu damuwa, domin kuwa ranar da gaskiya ta bayyana ga mai kin ka, zai gane cewa shi ne ke cikin kuskure ba kai ba.
Tubali na biyu ko kuma mu ce sinadari na gaba da za mu nazarta shi ne, rashin kamewa. Rashin kamewa a nan muna nufin rashin mutunci. Ke nan, duk mutumin da ya zabi ya kasance marar kamewa ga aikata abubuwan da ba daidai ba, shi ne marar mutunci, mai mummunan aiki. Babu shakka, duk wanda ya lizimci aikata ayyukan da ya san cewa ba daidai ne ba, abubuwan da kowa ya yi ittifakin cewa sun kauce wa addini da al’ada, to lallai kam ya zabi hanyar da ba za ta kai shi ga tudun mun tsira ba. Da sannu zai kasance marar mutunci ga kansa da iyalansa da kuma kabilarsa. Babu abin da ya kai mutunci kima a idon al’ummar da suka san mutuncin kansu. Dalili ke nan ma Hausawa suka ce, mutunci madara ne, idan ya zube shi ke nan. Ya kamata mu kare mutuncinmu, mu kasance masu kamewa daga zubar da mutuncinmu, mu kasance mutanen kwarai, abin alfahirin kanmu, al’ummarmu da kuma iyalinmu.
Wani tubali na gaba da za mu duba shi ne, gardama marar dalili, ko kuma yin gardama marar hujja, wacce ba ka da tabbataccen dalilin yin ta. Ba sai an kai ruwa rana ba wajen fahimtar wannan bayani, domin kuwa ita gardama marar dalili guba ce mai halakar da mai yin ta. Ana yin gardama ne idan ana son kawo gyara, idan kuma mutum yana da hujja mai karfi wacce za ta kawo gyara da fahimta. Amma duk lokacin da ka ce za ka yi gardama marar dalili, marar hujja, to maimakon ka kawo gyara, sai ma dai ka kawo rudu da rashin fahimta cikin al’umma. A irin wannan yanayin, duk mutumin da ya tsiri yin gardama marar dalili, shi ke jawo tashin hankali da husuma.
Domin dacewa da cin gajiyar gardama, sai mu tabbatar da cewa ga dalilin da ya sanya za mu yi gardama, kuma dalilin ya kasance na kawo fahimta da gyara ga al’ummarmu. Idan mun samu dalilin yin gardama mai hujja, sai kuma mu tanaji ilimi da kuma ingantattar hujjar da za ta ba mu natsuwa da bayanan da za mu bayyana domin fahimtar da abokan gardamar ta mu. Wannan zai sanya mu kasance masu mutunci, masu hikima da basira, wajen kawo gyara da fahimta ga al’umma.
Sinadarinmu na yau kuma na hudu a wannan tsari shi ne, illar tantiranci. Tantiranci abin gudu ne, abin kyama ne, abin gudu ne ga mutanen kirki. Me ake kira da tantiranci? Wasu na kiran tantiranci da shakiyanci, ballagazanci ko kuma gadara. Mutum yana ji yana gani ya zama marar kunya, marar tsoron aikata abin assha. Wannan mummunar dabi’a ce, dabi’a ce wacce ke dusashe kwarjini da mutuncin duk mai aikata ta. Da sannu za ka ji ana alakanta tantiri da muggan sunaye marasa dadin ji ga mai kamala. Idan ka ji ana cewa wane mugu ne shi, marar arziki ne, shakiyi ne; to lallai ya tabbata mai aikata tantiranci.  Idan har muna son tsira da mutuncinmu, kuma muna son gamawa da duniya lafiya; idan har muna son mu kasance na kwarai a cikin al’ummarmu, to ya dace mu kaurace wa tantiranci, mu daina yin duk wani abu da bai dace ba.
Darasinmu na yau dai, kamar yadda muka warware su, mun nuna wasu tubala ne guda hudu da muka ce ya kamata mutum ya guji aikata su. Wadannan abubuwa kuwa kamar yadda muka zayyana a sama, su ne karya, rashin kamewa, yin gardama marar hujja da kuma tantiranci. Wadannan muggan sinadarai ne da ke lalata mutum, rashin aikata su kuwa na sa martaba da mutuncin dan Adam ya daidaita. Wanda duk ya kaurace musu kuwa, zai zama mutumin kirki, abin darajawa ga daukacin al’umma. Allah Ya sanya mu dace da kyakkyawar rayuwa, amin. Sai kuma mun hadu a mako mai zuwa, inda za mu kawo muku wasu sinadaran na rayuwa. Allah Ya kai mu lafiya, amin.