Masana’antar shirya fina-finai ta Kasar Indiya Bollywood ta fitar da jerin wasu fina-finai da suka samu gagarumar riba a shekarar da muke bankwana da ita.
Duk da yadda cutar coronavirus ta targada tattalin arzikin duniya, wanda ya shafi kowane bangare na rayuwa ciki har da masana’antar ta Bollywood.
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- An cafke wadanda suka shirya casun jima’i a Kaduna
- An daure shi a gidan yari saboda zagin tutar China
Ga jerin fina-finan da suka ci riba:
- Fim din ‘Tanhaji’ wanda kamfanin Ajay Devgn FFilms T-Series ya shirya shi kuma kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dalar Amurka miliyan 52.
- Fim din ‘Baaghi 3’ wanda kamfanin Nadiadwala Grandson Entertainment Fox Star Studios ya shirya shi kamfanin Fox Star Studios ya yi dillancinsa ya samu Dala miliyan 19.
- ‘Street Dancer 3D’ wanda kamfanin T-Series Remo D’Souza Entertainment ya shirya shi kuma kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan14.
- ‘Shubh Mangal Zyada Saavdhan’ wanda kamfanin T-Series Colour Yellow Productions ya shirya shi kuma kamfain AA Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan.
- ‘Malang’ wanda kamfanin T-Series Luv Films Northern Lights Entertainment ya shirya shi kamfanin Yash Raj Films ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 12.
- Fim din ‘Chhapaak’ wanda kamfanin Fox Star Studios Productions Mriga Films ya shirya, Fox Star Studios ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 7.8.
- ‘Love Aaj Kal’ wanda kamfanin Maddock Films Window Seat Films Jio Studios Reliance Entertainment ya shirya shi, kamfanin Pen Marudhar Entertainment ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 7.4.
- ‘Jawaani Jaaneman’ kamfanin Pooja Entertainment Black Knight Films Northern Lights Films ya shirya shi, kamfanin Pen Marudhar Entertainment ya yi dillancinsa ya samu kudi Dala miliyan 6.3.
- ‘Thappad’ wanda kamfanin T-Series Benaras Media Works ya shirya shi, kamfanin AA Films ya yi dillancinsa ya samu Dala miliyan 6.2.
- Fim din ‘Panga’ wanda kamfanin Fox Star Studios ya shirya shi, kuma ya yi dillancin kayansa, ya samu Dala miliyan 5.8.