✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu dai a samu wutar lantarki!

A Larabar makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauki kwakkwaran mataki kan shirinta na inganta da kuma samar da wutar lantarki a Najeriya,…

A Larabar makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauki kwakkwaran mataki kan shirinta na inganta da kuma samar da wutar lantarki a Najeriya, wanda hakan ne ya sanya ta mika lasisi da satifiket din mallakar hukumar samar da wutar lantarki (PHCN) ga wadansu kamfanonin samar da wutar lantarki masu zaman kansu. A lokacin bikin wanda aka gudanar a Abuja Shugaba Goodluck Jonathan ya mika takardun ga kamfanoni shida masu samar da wutar lantarki da ake kira (gencos) da kuma kamfanoni tara da suke rarraba wutar da ake kira (discos), wanda da ma dukkan wadannan kamfanoni an cire su ne daga hukumar PHCN. Kuma jimmilar wadannan kamfanoni 15 sun gama biyan kudinsu.
A cikin kamfanoni da suka karbi satifiket da lasisin akwai kamfanin Mainstream Energy a karkashin jagorancin Kanar Sani Bello, wanda shi ne ya mallaki tashar wuta ta Kainji Dam da kuma ta Jebba, inda Femi Otedola mai kamfanin Amerion Power ya mallaki tashar wuta ta Geregu, Tony Elumelu mai kamfanin Transcorp/Woodrock Consortium ya mallaki tashar wuta ta Ughelli, Jihar Delta. A cikin kamfanonin discos kuma akwai kamfanin West Power and Gas (Eko discos) da NEDC/KEPCO (Ikeja) da 4Power Consortium  (Fatakwal) da bigeo Consortium (Benin) da Aura Energy (Jos) da Kann Consortium (Abuja) da Integrated Energy (Ibadan da Yola) da kuma Sahelian Power (Kano).
Sai dai jim kadan da bayar da lasisi da satifiket din sai aka fara korafe-korafe a kan an sayar da hukumar wutar arha, inda aka sayar da ita Naira biliyan 404, bayan kuma gwamnati ta kashe fiye da Naira tiriliyan 3.2 cikin shekara 14 wurin gyara da inganta wutar lantarki a kasar nan. Kwamitin neman karin bayani na Majalisar Wakilai ta tarayya a shekarar 2008-9 sun gano gwamnatin Obasanjo ta kashe kusa da Dala biliyan 16 a kan hukumar wutar lantarkin. Hakan ya sanya tsohon shugaban kasa marigayi ’Yar’aduwa ya ce ‘bai haifar da da mai ido’ ba. Ba a jima ba sai gwamnatin ’Yar’aduwa/Jonathan ta fitar da Dala biliyan 5 don inganta wutar lantarki, wanda kuma fiye da rabin kudin an ciro ne da asusun ajiya na rarar mai. Kodayake ‘Yar’aduwa ya tuntubi gwamnatin jihohi da na kananan hukumomi ba kamar yadda Obasanjo ya fitar da kudin ba tare da masaniyarsu ba.
Duk da wadannan kudaden da aka kashe baya ga wadanda ake fitarwa a lokacin kasafin kudi, ba a magance matsalar wutar lantarki ba, za a iya cewa gara jiya da yau, domin a yanzu ba a samar da wutar da karfinta ya kai megawat dubu 6, abin takaicin shi ne wutar da ake samu a kasar nan bai kai daya bisa goma na wutar da ake samu a Afrika ta Kudu ba, wanda yawan jama’a a kasar nan ya ninka na Afrika ta Kudu sau uku.
A wannan halin da aka cika kasar nan da kamfen din a zuba hannun jari a harkar samar da wutar lantarki, sai ga shi an damka hukumar a hannun wadansu, akwai yiwuwar hakan ba zai haifar da da mai ido ba. A yanzu dai za a iya cewa makudan kudaden da aka kashe wajen inganta wuta a kasar nan babu su babu dalilinsu, muna fata Hukumar EFCC da ICPC  da sauran hukumomi za su daura damara wurin ganin an kwato kudaden tun da har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Sannan ya kamata a hukunta wadanda suka yi sama da fadi da kudaden.  Abin fata dai shi ne tun da an damka hakkin samar da wutar lantarki a hannu kamfanonin gencos da discos da kuma wani kamfanin kasar Kanada, Allah Ya sa wadannan kamfanonin su fitar da jaki daga cikin duma, kamar yadda kamfanonin sadarwa masu zaman kansu a kasar nan suka yi lokacin da aka damka musu ragamar sadarwa.
Wani abin damuwa shi ne idan aka cire abin da kamfanonin sadarwa masu zaman kansu suka yi lokacin da aka ba su ragamar hakkin inganta sadarwa, babu wadansu kamfanoni a bangarori mabambanta tun shekarar 2000 da suka samu nasara bayan na sadarwa. Don haka ya kamata a sa ido a kan wadannan kamfanonin da ke samar da wutar.
Idan wadannan kamfanoni suka zage damtse wajen fitar da karin da radadinsa ya addabi harkar wutar lantarki, to tattalin arziki zai inganta, kuma ’yan Najeriya za su ji dadi.
Yanzu dai za a iya mantawa da duk wani batu idan wutar lantarki za ta inganta. Mu dai kawai a samu wutar lantarki.