✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Motocin yaki kirar Najeriya sun inganta yaki da Boko Haram

Sojoji sun samu karin kuzarin murkushe ta’addancin Boko Haram, ISWAP da sauransu.

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce motocin yaki da rundunar ke karewa sun kara mata kuzarin murkushe kungiyar Boko Haram da ISWAP.

Buratai ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da shirin tallafin ofishinsa, cibiyar hada motoci da, masana’antar kere-kere ta zamani da kuma masaukin dakaru da za su tafi filin daga a Kaduna.

“An riga an kaddamar da ‘EZUGWU’ guda takwa a ayyukan rundunar Operation LAFIYA DOLE da Operation SAHEL SANITY.

“Motocin sun kara mana karfin yakar Boko Haram da ISWAP”, inji Buratai wanda Kwamandan Kwalejin Horas da Kanana Hafsoshin Soji (NDA), Manjo Janar Jamil Sarham ya wakilta.

Ya ce, “Sauran kayan soji da ake kerawa da wannan hadin gwiwar sun hada kananan motocin yaki, motocin sintiri na musamman, motar gasa biredi ta tafi-da-gidanka, moatar haka rijiyar burtsatsai ta tafi da gidanka da sauransu.

“A takaice wadannan cibiyoyin na taimaka wa Rundunar Sojin Kasa zartar a ayyukanta a dukkannin bangarorin yaki da ta’addanci a Arewa maso Gaba da sauransu”, inji Buratai.

Kwamandan cibiyar, Sunday Araoye, ya ce samun sabbin fasahohin kere-keren za su taimaka musu wurin samar da kayan yaki na zamani da za su gogayya a ko’ina a duniya.