✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motoci sun ki tafiya da daliban Najeriya bayan an yi lodi a Khartoum

Bayan dalibai da sauran ’yan Najeriya sun hau motoci an gama lodi, sai direbobin suka ce babu inda za su motsa da motocin sai gwamnatin…

Ragowar ’yan Najeriya da ke Sudan sun ga ta-leko-ta-koma, inda motocin da aka tura su kwaso su bayan barkewar yaki, suka sauke su a yayin da ake jiran tashin motocin.

A ranar Asabar, bayan dalibai da sauran ’yan Najeriya sun hau motoci an gama loda kayansu, sai direbobin suka ce babu inda za su motsa da motocin sai gwamnatin Najeriya ta biya su kudin aikin.

Daya daga cikin daliban da abin ya shafa, ya shaida wa Aminiya ce, “Cikin ikon Allah jiya (Asabar) har mun shiga mototoci, don sun kawo mana baki daya har da extra ma.

“Amma kuma har za mu fara tafiya sai suka ce gwamnati ba ta biya su kudadensu ba; Shi ya sa suka ce ba za su tafi ba sai an biya su.

“Amma kayanmu suna cikin motar kuma su ma mototocin suna nan; an ce dai In sha’a Allah yau (Lahadi) bayan asuba za mu tafi.”

A ranar Lahadi wa’adin da bangarori masu yaki da juna a Sudan na tsagaita wuta domin kwashe ’yan kasashen waje da ayyukan jin kai yake karewa.

Iyaye na newa ma ’ya’yansu mafita

Aminiya ta ruwaito cewa iyayen daliban da suka makale a iyakar kasar Masar bayan sun bar Sudan suna duba yiwuwar ’ya’yan nasu su koma birnin Port Sudan na kasar, ko za su samu jirgi zuwa Najeriya.

Yakin da ake fama da shi a Khartoum ya sa an rufe harkokin jiragen sama, amma duk da haka, kawo yanzu ana ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Port Sudan.

A kan haka ne iyayen daliban da suka kwana uku a kan iyakar kasar Masar ba su samu izinin shiga ba saboda rashin takardu, suke ganin maimakon jiran gawon shanu, gara su nema wa ’ya’yan nasu mafita ta Port Sudan.

Suna kyautata zaton cewa a Port Sudan za a samu jirgin da zai kwaso ’yan Najeriya zuwa gida, ga shi babu bukatar takardun da suka hana su tsallakawa zuwa kasar Masar.

Gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe ’yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Sudan a motoci zuwa Alkahira, babban birnin kasar Masar, inda daga nan za a dauke su a jirgi zuwa gida.

Sai dai tun ranar Alhamis rukunin farko na ’yan Najeriyar da aka kwaso daga Khartoum, fadar kasar Sudan suka isa iyakar kasar Masar da ke Aswan, amma hukumomi sun hana su izinin tsallakawa saboda rashin takardun da ya kamata.