✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mohammed Salah ya ji rauni

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Liberpool na Ingila sun ce dan kwallon gabansu Mohammed Salah ya ji rauni a wasan da kulob din…

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Liberpool na Ingila sun ce dan kwallon gabansu Mohammed Salah ya ji rauni a wasan da kulob din ya yi da Manchester City a gasar Zakarun Turai a shekaranjiya Laraba.

A wasan, Liberpool ce ta lallasa Manchester City da ci 3-0 kuma Salah ne ya fara zura kwallon farko.

Sai dai jim kadan bayan an koma hutun rabin lokaci ne Salah ya ji rauni, al’amarin da ya sa aka canja shi.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Salah ba zai yi wasa karo na biyu da City ba a ranar Talata mai zuwa, kuma hakan ba karamin koma-baya ba ne ga kulob din na Liberpool.

Sai dai kulob din Liberpool bai bayyana takamaiman lokacin da dan kwallon zai koma fagen wasa ba.

Kawo yanzu Salah ne kan gaba a gasar rukunin Firimiyar Ingila bayan ya zura kwallo 29 a raga.  A kakar wasa ta bana ya zura kwallo 39 a dukan wasannin da ya yi wa Liberpool da hakan ta sa tauraruwarsa ke haskakawa.

Masana harkar kwallo na ganin Manchester City za ta iya amfani da wannan dama ta rashin Salah wajen fanshe kwallaye ukun da Liberpool ta zura mata a raga.

Yanzu dai masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wasan zai kaya a  ranar Talata mai zuwa idan Allah Ya kai mu.