✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mohammed Salah ne ya lashe Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC

Shahararren dan kwallon Masar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.  A ranar Litinin da ta wuce…

Shahararren dan kwallon Masar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.  A ranar Litinin da ta wuce ne kafar watsa labaran BBC ya sanar da sakamakon gasar.

’Yan kwallo biyar ne suka fafata a kokarin lashe wannan gasa da suka hada da Mohammed Salah dan asalin Masar da  Pierre-Emerick Aubameyang, dan asalin Gabon da Naby Keita dan asalin Gini da Sadio Mane dan asalin Senegal da kuma bictor Moses dan asalin Najeriya.

A duk shekara ce gidan rediyon BBC yake shirya irin wannan gasa ga ’yan kwallon Afirka da ke buga kwallo a sassan duniya inda suke ba jama’a musamman masoya kwallon kafa dama wajen kada kuri’a don zabar Gwarzon dan kwallon.

Mohammed Salah, wanda tauraruwarsa ke haskakawa a bana, ya zuwa yanzu shi ne dan kwallon da ya fi  yawan zura kwallaye a gasar rukunin firimiyar Ingila bayan ya zura kwallaye 13.

Haka kuma Salah ne ya taimakawa Masar hayewa gasar cin kofin duniya a Rasha a karon farko tun bayan shekarar 1990 da hakan ta sa aka zabe shi.