✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyetti Allah Kautal Hore ta bukaci a kawo karshen kisan kare dangi da ake wa Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta bukaci lallai Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo domin ta kawo karshen kisan kare-dangi da ake yi wa Fulani…

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta bukaci lallai Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo domin ta kawo karshen kisan kare-dangi da ake yi wa Fulani makiyaya a kasar nan, kana kuma ta hukunta   wadanda aka samu da hannu wajen yi wa makiyaya kisan kare dangi.

Alhaji Gidado Idris, shugaban kungiyar na Arewa ta takiya ne ya bukaci haka, a zantawarsu da Aminiya. Ya ce a jihohin Adamawa, Taraba da kuma Filato an yi wa Fulani makiyaya kisan gilla.

Shugaban kungiyar, wanda ya ziyarci Jihar Kurosriba domin bin bahasin rikicin da aka yi kwanan baya tsakanin matasan Ugaga da ke karamar Hukumar Yala, inda aka kashe mutum daya aka cire masa kai, mutum biyu kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

“Alhalin bincike ya nuna matasan Ugaga su ne suke bin makiyaya daji su kai masu farmaki, su kashe masu shanu su kwashe naman, su kuma makiyayan idan sun ki yarda da satar sai su yi masu kwanton bauna su sare su kamar yadda suke yi a kananan hukumomin Bekwarra da Yala kuma abun damuwar, idan ma sun kashe sai su datse kan a rasa inda suka yi da shi, sai gangar jiki suke bari,” inji shi.

Shugaban ya ci gaba da kokawa da irin duk wani wulakanci da ake yi wa Fulani amma Gwamnatin Tarayya ta yi kemudugus da hana kisan kare dangin da ake masu da kuma satar shanu. “Magana ta gaskiya ni ba na jin dadin irin yadda idan aka kashe Bafulatani ake datse masa kai da ma sauran wasu sassan jikinsa a ta fi da su. Misali, kamar yadda ya faru a karamar Hukumar Bassa, Jihar Filato, inda aka kashe mana Fulani aka datse kawunansu, ba mu gani ba har yau har kuma gobe,” inji shi.

Da yake yin tsokaci game da dokar hana kiwo da Gwamnatin Jihar Binuwai ta kafa, a nan sai shugaban ya ce: “Na san duk wannan siyasa ce, domin masu adawa da mulkin gwamna jihar ne suke zuga shi, don ba su kaunar ya yi wasu shekara hudu yana mulkinsu. Kana kuma nan da sabuwar shekara ma Gwamnatin jihar Taraba ma ta ce za ta aiwatar da doka irin wannan.”

Ya danganta matsalar da Fulani ke fuskanta ta karancin burtali da gwamnatoci matakin jiha har zuwa tarayya da suka auna suka yi wasu bukatu nasu ya kawo karancin burtali. “Amma a ce Bafulatani ya ajiye saniya ya samar mata da wurin kiwo ko ya rika nemo mata abin da za ta ci ai takurawa ce wannna.”

Daga karshe ya koka da babbar murya cewa: “Ni ba na jin dadin irin yadda Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari take yin kawaici ake kisan Fulani makiyaya ba tare da ta dauki wani matakin hana hakan ba, alhali ga mayakan sa-kai na yankin Neja-Delta nan ko yaya suka motsa gwamnati na share masu hawaye, kana kuma ga ’yan Biyafara su ma sai lallashinsu ake yi amma kisan Bafulatani da yi masa kare-dangi ya zama abin a yi biris da shi. Muna fata al’amarin zai kawo karshe, mu samu zaman lafiya.”