✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan man fetur ya sayi fom din neman takarar shugaban kasa a APC

Mun siya masa fom din takara saboda kwazonsa a Ma'aikatar man fetur ta Najeriya.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga sahun masu neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a kasar.

Wata kungiyar magoya bayansa mai suna ‘Good People of Nigeria’ ce ta sayi fom din neman takarar a madadin ministan.

Da take jawabi a gaban Babban Ofishin Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC da ke Abuja, kungiyar ta ce ta saya wa tsohon gwamnan na Jihar Bayelsa fom din takarar ne duba da kwazonsa a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta kasar.

Jagoran kungiyar, Alhaji Mohammed Abu, ya ce hakan ne ya sanya suka ga cancantar ya gaji kujerar Shugaba Kasa Muhammadu Buhari.

Mista Sylva ya mallaki fom din neman takarar a yayin da a ‘yan kwanakin nan ake fama da matsalar karancin man fetur musamman a wasu manyan birane na kasar ciki har da Abuja.

A kwanaki ukun da suka gabata, ‘yan Najeriya kan shafe sa’o’i suna bin layin shan man fetur a gidajen mai, matsalar da Kamfanin na NNPC ya jingina ga tafiyar hawainiya da ake yi wajen dauko dakon man fetur din daga daffonsa.