’Yan sa’o’i bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, daya daga cikin Ministocin da ke hankoron takarar Shugaban Kasa kuma Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajiuba ya ajiye aiki.
Bayanin hakan ya bulla ne a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ranar Laraba, inda bayanai ke nuna ya ajiye mukamin ne domin ya mayar da hankali kan takarar da yake yi.
Emeka Nwajiuba guda ne cikin Ministocin shidan da suka sayi fom din takarar Shugaban Kasa na Naira miliyan 100 a APC, gabanin zaben fid da gwani na jam’iyyar da za a gudanar a karshen watan Mayun 2022.
Sauran Ministocin da ke neman wannan kujera sun hada da na Sufuri Rotimi Ameachi, da na Neja Delta,, Godswill Akpabio, da na Kwadago, Chris Ngige.
Kazalika, akwai na Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, da Minista a Ma’ikatar man Fetir, Timipere Sylvia.
Idan dai ba a manta ba Shugaba Buhari ya ba wa duk wadanda ke rike da madafun iko, kuma ke son takara wa’adin nan da ranar Litinin domin su ajiye aiki.