✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista: Zan bai wa masu suka ta mamaki —Matawalle

Matawalle ta ce zai bai wa mara da kunya.

Karamin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya sha alwashin bai wa masu sukar sa mamaki.

Wasu mutane sun caccaki mukamin minista da aka bai wa Matawalle, inda suke ganin tsohon bai taɓuka abun a zo a gani ba a lokacin da yake gwamnan Zamfara.

Sai dai Matawalle ya ce yana da yaƙinin cewa zai iya aiwatar da aikin, kuma zai yi aiki tuƙuru don ganin an tabbatar da tsaro a ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen liyafar da aka shirya masa a Abuja, Matawalle ya ce, “Na sha jin wasu mutane suna cewa yayana Badaru (Babban Ministan Tsaro) da kuma ni ba mu cancanci zama ministocin tsaro ba, waɗannan mutane ma ba su fahimci me ke faruwa ba.

“Saboda haka, ba a nan matsalar take ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne jajircewa.

“Lokacin da nake Gwamnan Zamfara mun ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron jihar.

“Akwai lokacin da muka yi kwanaki 100 ba tare da wani ƙalubalen tsaro ba.

“Mun kuma shafe watanni tara ba tare da an cutar da ko mutum daya ba.

“Dukkan matakan da na ɗauka na daƙile matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, dole ne na fara aiwatar da su, sannan sauran gwamnonin sun bi sawu.

“Wannan shi ne abin da ya dace saboda ina da kyakkyawar fahimta game da al’amuran tsaro.

“Ina da albishir ga al’ummar Jihar Zamfara cewa ba zan ba su kunya ba.

“Na yi imanin cewa da taimakon Allah, za mu iya shawo kan matsalolin tsaro.

“Masu cewa ni da Badaru ba za mu iya ba, za su ji kunya. Za su ga cewa Allah Ne ke yin aikin ba su ba.”

Ya kara da cewa, “A da, muna neman taimako. Amma yanzu, muna matakin da mu za mu bai wa wasu taimako.”