Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub, ya bukaci kamfanin da ke aikin sake gina titin Kano zuwa Kaduna da ya kammala shi nan da karshen shekarar 2022.
Ya kuma bukace su da su kara azama wajen ganin sun kammala ragowar na Kaduna zuwa Abuja a cikin watanni uku na farkon 2023.
Ministan ya bayyana haka ne ranar Asabar, lokacin da yake duba sashe na uku na aikin titin wanda ya tashi daga Kano zuwa Zariya.
Ministan ya kuma ce, “Wannan titin da wuya ka samu mai muhimmancinsa a Najeriya, don shi galibin jihohin Arewacin Najeriya ke bi zuwa wasu sassan kasar, har ma da wucewa wasu makwabtan kasashe irinsu Nijar da Chadi.
“Kusan duk wanda ya fito daga wadannan yankunan zai je Abuja ko Kudancin Najeriya, dole sai ya bi ta wannan hanyar.
“Saboda haka, duk idon jama’a na kanmu wajen ganin mun kammala shi a kan lokaci. A kan haka, na umarci kamfanin da yake aikin da ya tabbatar ya kammala sassa biyu [Kano zuwa Zariya da Zariya zuwa Kaduna], alabasshi a watanni ukun farkon shekarar 2023 su tabbatar an kammala har zuwa Abuja.
“Wani abu kuma da kamfanin ya fada min yana yi kuma na gani shi ne yadda yake nika tsohuwar kwaltar ya kara mata sinadarai sannan ya sake amfani da ita.
“Sun ce wannan shi ne karo na farko da aka fara amfani da fasahar wajen gina hanya a Najeriya. Wannan ya birge ni sosai, kuma na gamsu da ingancin aikin da suke yi.
“Na kuma roki kamfanin da su kara yawan mutanen da suke diba aiki, sannan musamman su rika dibar matasa masu yi wa kasa hidima da wadanda suka kammala karatu a cikin ma’aikatan nasu,” inji Ministan.
Umar EL-Yakub ya kuma roki mutane da su daina ajiye ababen hawa ko yin sana’o’i a gefen titin da ake aikin don kauce wa jefa rayukansu cikin hatsari.
Ya kuma ce za a gina gadojin masu tsallaka titi da dama don kaucewa yawan samu hadura, inda ya ce, “ko a tsakanin Zariya zuwa Kaduna za mu yi irin wadannan gadojin akalla guda bakwai.”
Shi ma kamfanin ya ce zai yi iya kokarinsa don ganin ya kammala aikin kamar yadda aka bukata.
A cewar wakilin Injiniyan kamfanin, Injiniya Ibrahim Nmadu, tun bayan fara aikin, sun debi mutum akalla 1,500 ayyuka daban-daban.
Idan za a iya tunawa, an ba kamfanin Julius Berger kwangilar titin mai nisan sama da kilomita 400 daga Kano zuwa Abuja a watan Disambar 2017, inda ya fara aikin a watan Mayun 2018.