Minista a Ma’aikatar Ciniki da Zuba Jari, Ambasada Maryam Katagum ta yanke jiki ta fadi tana tsaka da wata ziyarar aiki a Jihar Bauchi.
Rahotanni sun ce nan take aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH) domin samun kulawar gaggawa.
Ministar dai ta je Bauchi ne domin kaddamar da wani shirin tallafawa jama’a a daya daga cikin manyan kantina a Bauchi, amma kwatsam sai ta yanke jiki ta fadi a daidai lokacin da take kokarin gabatar da jawabi.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad da Mataimakinsa, Sanata Baba Tela da sauran manyan mukarraban gwamnati na wurin a lkocin da lamarin ya faru.
Wani ganau a inda lamarin ya faru ya shaida wa wakilin Aminiya cewa Miniosta Maryam ta fadi ne a daidai lokacin da ta mike don gabatar da jawabi.
“Kawai gani muka yi ta dafe kanta ta fadi a kasa, amma an samu an garzaya da ita zuwa asibiti cikin gaggawa,” inji shi.
Wani babban jami’in gwamnatin Jihar ya sahidawa ’yan jarida cewa da zarar ta sami sauki za a mayar da ita Abuja domin ta ci gaba da samun kulawa.
Tuni dai rahotanni suka ce an garzaya da ministar zuwa sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na asibitin koyarwar na ATBU.
Kazalika, wata majiya a asibitin wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce Shugaban Asibitin, Dokta Yusuf Jibrin ne da kansa ya garzaya da ita zuwa sashen.
“Rashin lafiyarta ba wata gagaruma ba ce, kuma Shugaban asibitin ne da kansa ya tukata a motarsa zuwa sashen domin a kula da ita,” inji majiyar.
Sai dai duk kokarin wakilin Aminiya na jin ta bakin Ma’aikatar Kasuwancin kan yanayin lafiyar ministar ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.