✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi ya ki yarda da tayin Valencia

Kyaftin din Najeriya da ke buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo John Obi Mikel ya ki amincewa da tayin da kulob din balencia…

Kyaftin din Najeriya da ke buga wa kulob din Chelsea na Ingila kwallo John Obi Mikel ya ki amincewa da tayin da kulob din balencia na Sifen ya yi masa na biyansa albashin Yuro miliyan 3 kwatankwacin Naira biliyan daya da rabi a shekara idan ya amince ya koma kulob din. 

balencia dai tana kokarin saye Mikel ne a watan Janairun 2017 idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.
Sai dai John Obi Mikel ya ki amincewa da wannan tayin inda yake neman kulob din ya biya shi albashin Yuro miliyan 10 kwatankwacin Naira biliyan 5 da miliyan 100 a shekara.
Hakan ta sa dan kwallon ya fara yunkurin karkata akalarsa zuwa Nahiyar Asiya don samun kulob din da zai cigaba da yin kwallo a can.
Mikel dan kimanin shekara 29 watanni shida suka rage kwantaraginsa ta kare da kulob din Chelsea kuma ga dukkan alamu kulob din ba zai sabunta masa kwantaragi ba.
Kulob da dama sun shiga zawarcin Mikel tun bayan da suka fahimci kwantaraginsa ta kusa karewa da kulob din Chelsea. Ana sa ran dan kwallon zai samu kulob a Ingila idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan Janairun badi.