Wani magidanci dan shekara 47 ya gurfana a gaban kotu bisa zargin lakada wa matarsa mai juna biyu dukan tsiya har sai da ta mutu.
Bayan dukan da mutumin ya yi wa matar tasa mai suna Blessing har ta mutu tare da abun da take dauke da shi ne aka gurfanar da shi a kotu.
Magidancin ya yi aika-aikan ne a cikin watan Afrilu a gidansu da ke kan titin Oke-Agba a birinin Akure.
Dan sanda mai shigar da kara Insfekta Uloh Goodluck ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba wa sashe na 319, karamin sashe na daya na kundin manyan laifuffuka na jihar ta Ondo.
Ya kuma bukaci kotun da ta umarci a ci gaba da tsare mutumin har ya zuwa lokacin za a yanke masa hukunci la’akari da girman laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Lauyan wanda ake zargi, A. Ololike bai ja da bukatar dan sanda mai shigar da karar ba.
Daga nan ne kuma alkalin kotun, Mai Shari’a N. T. Aladejana ya umarci a ci gaba da tsare Mista Olabode har zuwa lokacin da za a yanke masa hukuncin.
Kotun da dage sauraron shari’ar zuwa ranar takwas ga watan Satumba mai kamawa.