✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Micheal Carrick zai yi ritaya

Kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United na Ingila Micheal Carrick ya bayyana aniyarsa ta yin…

Kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United na Ingila Micheal Carrick ya bayyana aniyarsa ta yin murabus daga yin kwallon kafa a karshen kakar wasa ta bana.

Carrick mai shgekara 36, ya buga wa kulob din United wasa 463  bayan ya koma kulob din daga Tottenham a shekarar 2006 a kan Fam miliyan 18.  Haka kuma ya yi wa kasar haihuwarsa Ingila wasa har sau 34 kawo yanzu.

“Akwai lokacin da dan kwallo zai ji a jikinsa lokacin yin ritayarsa ya yi, to haka nake ji a yanzu, don haka na yanke wannan shawara”, inji shi.

Sai dai Carrick ya nuna sha’awar horar da kulob din United idan ya samu damar yin haka da zarar ya yi ritayar.

A watan Janairu ne kocin United Jose Mourinho ya ce zai yi maraba da Carrick a matsayin daya daga cikin masu taimaka masa a matsayin koci idan dan kwallon ya yi ritaya.  Masana harkar kwallo suna ganin akwai yiwuwar Carrick ya zama koci a United idan ya daina buga wa kulob din kwallo.

Rahotanni sun nuna Mieheal Carrick dai yana fama da matsalar ciwon zuciya da hakan ta sa kawo yanzu wasa hudu kacal ya yi wa United a kakar wasa ta bana.