✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya taba samun jan kati kuwa?

Wannan ita ce tambayar da wadansu masoya kwallon kafa suka yi mini a lokacin da suke musun kwallo a kan ko Lionel Messi ya taba…

Wannan ita ce tambayar da wadansu masoya kwallon kafa suka yi mini a lokacin da suke musun kwallo a kan ko Lionel Messi ya taba samun jan kati (Red Card) a tarihin kwallonsa?.  Hakan ta sa na yi bincike kuma na samu amsar tambayar tasu kamar haka:
Shahararren dan kwallon Ajantina da FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya taba samun jan kati (Red Card) sau daya a rayuwarsa.   Ya samu jan katin ne a lokacin da kasar haihuwarsa Ajantina take yin kwallo da Hungary a shekarar 2005.  Rahoton ya nuna Messi ya samu jan katin ne minti biyu kacal da shigarsa fili bayan kocin Ajantina ya sanya shi wasa.  Yanzu kimanin shekara 11 kenan da wancan al’amari ya faru da Messi kuma tun daga wancan lokaci kawo yanzu dan kwallon bai sake samun jan kati ba.  Sai dai ya samu katin gargadi (Yellow Card)  a lokuta daban-daban don ko a ranar Asabar da ta gabata sai da dan kwallon ya samu katin gargadi a wasan da FC Barcelona ta yi da Espanyol a gasar rukunin La-Liga na Sifen.
Messi dai an shaide shi a matsayin mai saukin kai da hakan ta sa ba ya cacar baki da alkalin wasa ko dan kwallo.  A mafi yawan lokuta shi ake yi wa keta al’amarin da ya sa yake janyo wa ‘yan kwallo jan kati ko katin gargadi.
Lionel Messi shi ne Gwarzon dan kwallon duniya a halin yanzu, da hakan ta sa ya lashe kyautar sau biyar kuma ba a samun dan kwallon da ya kama kafarsa ba wajen lashe wannan kyauta kawo yanzu ba.