Dan kwallon FC Barcelona na Spain, Lionel Messi, ya sake kafa sabon tarihi a Gasar La-Liga ta Spain bayan da ya zura kwallo a ragar Sebilla a bugun tazara. Wannan kwallo ta kasance ta 420 a wasanni 455 da ya yi a gasar.
Barcelona ta zura kwallaye 4-0 ne a ragar Sebilla a ranar Lahadin da ta wuce.
Yanzu Messi ya doke abokin takararsa Cristiano Ronaldo da ke da yawan kwallaye 419.
Ana duba ’yan kwallon da suka fi yawan zura kwallaye ne a gasanni biyar a Turai da suka hada da Firimiya a Ingila da La-Liga a Spain da Serie A a Italiya da Ligue 1 a Faransa da kuma Bundesliga a Jamus inda yanzu Messi ya kasance na daya.
Sai dai Ronaldo da ke da yawan kwallaye 419 ya same su ne a gasanni daban-daban da suka hada da kwallaye 84 a kulob din Manchester United na Ingila da kwallaye 311 a kulob din Real Madrid na Spain da kuma kwallaye 24 a kulob dinsa na yanzu wato Jubentus na Italiya.
Sai dai komai zai iya faruwa a tsakanin Messi da Ronaldo ganin an shiga kaka ta bana kuma akwai yiwuwar ’yan kwallon za su ci gaba da zura kwallaye a raga.