✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya gana da dan-ga-ni-kasheninsa

A ranar Talatar da ta wuce ne Lionel Messi ya samu haduwa ido da ido da yaron nan Murtaza Ahmadi dan kimanin shekara 6 dan…

A ranar Talatar da ta wuce ne Lionel Messi ya samu haduwa ido da ido da yaron nan Murtaza Ahmadi dan kimanin shekara 6 dan asalin Afghanistan da ya zama dan-ga-ni-kasheninsa.

Messi ya gana da yaron ne a lokacin da kulob din FC Barcelona ya ziyarci katar don yin wasan sada zumunta da kulob din Al-Ahli na Masar inda Barcelona ta samu nasara a wasan da ci 5-3.
Yaron dan kimanin shekara 6 tun a watan Janairun wannan shekara ce aka baza hotunansa a yanar gizo bayan an ga yana kwallo a cikin sa’o’insa kamar Messi sanye da rigar leda irin ta Messi mai dauke da lamba 10.
Hakan ta sa yaron ya janyo hankalin duniya inda Hukumar kwallon kafa ta Afghanistan ta yi kokarin hada yaron da Lionel Messi tun a wancan lokaci amma hakan bai yiwu ba.
Sai dai a ranar Talata ce hakar yaron ta cimma ruwa bayan iyayensa sun kai shi katar inda ya gana da Messi ido da ido.
Lionel Messi ya nuna jin dadinsa da ya hadu da yaron da ke matukar kaunarsa kuma ya sha alwashin cigaba da karfafa wa yaron gwiwa a harkar kwallon kafa.
Tun kafin haduwarsu Messi ya aika wa yaron rigar kwallnsa ta ainihi mai dauke da lamba 10 don cigaba da karafa wa yaron gwiwa.