✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mene ne maganin da zan shafa wa billena ya bace?

Ni bafullace ne, an mini tsaga a fuska tun ina karami to amma ba na son ganinsa. Ko ya zan yi na magance shi? Akwai…

Ni bafullace ne, an mini tsaga a fuska tun ina karami to amma ba na son ganinsa. Ko ya zan yi na magance shi? Akwai man shafawa?

Daga Aminu B.K.

 

Amsa: Tsaga a fuska ko a jiki, na daya daga cikin al’adun mutanen Nahiyar Afirka, domin ba a san shi a kowace nahiya ba banda ta Afirka. Su mutanen wannan nahiya suna yi wa ‘ya’yansu ne a matsayin wani ado ko shaidar cewa wane kabila kaza ne. Sai dai dukkanin kungiyoyin lafiya da na sanin hakkin dan Adam sun yi ittifaki kan cewa tsaga jikin yara cin zarafi ne, tunda jarirai ba su da hurumin zabi a kan wannan. A kasar nan ma har sai da ta kasance cewa an sa wata doka kusan shekaru 15 da suka wuce, wadda ta nuna tsaga fuskar jariri cin zarafi ne, har ma dokar ta tanadi dauri ga duk wanda aka kama yana yi wa ‘ya’yansa irin wannan tsagu.

In dai aka riga aka tsaga fata haka irin na bille mai zurfi sosai, to yana da wahala man shafawa ya fitar da shi. Idan bai yi zurfi sosai ba, a wasu masu tsaga da dama akan samu idan suka kara shekaru zanen ya bace gaba-daya da kansa, bayan sun kai wasu munzali na shekaru kenan. A wasu kuma sai sun nemi wani man shafawa na musamman, wato man gyara tabo. A wadanda yake baro-baro mai zurfi, sai dai a ba su shawarar ganin likitan tiyatar fata, wato likitan kwalliya da akan kira plastic surgeon, wanda zai ga billen ya ba da shawarar abin da ya kamata a yi. Zai iya cewa hasken maganadison laser kadai za a yi amfani da shi, ko wani sinadarin mai cike fata, ko kuma ‘yar tiyata, duk don wajen ya dawo dai-dai.

 

Me ya sa lokutan sanyi jikina kan yawan yin kaikayi?

Daga Sani Umar, Malumfashi

 

Amsa: Lokacin sanyi ai yanayi ne busasshe, don haka ba abin mamaki ba ne a ce wannan kaikayin daga bushewar fata ne sakamakon shigowar hunturu. Don haka yin amfani da man shafawa mai danko ko mai danshi zai iya magance wannan.

 

Ni mai yawan cin goruba ne, domin wani lokaci ma idan na ci da yawa cikina kan murda. 

Daga Muhammad Lawal, Bauchi

 

Amsa: E, kamar sauran ‘ya’yan itatuwa goruba tana da sinadari na wankin ciki da akan kira fibre, irin wanda ake samu kamar a tikar aya. Idan ta yi yawa takan murda ciki. Don haka duk da ana so mutum ya rika cin ‘ya’yan itatuwa a kullum, ba a ce kala daya zai rika ci kadai ba – ana so a kullum a rika samun wani abu daban, ba a sa kala daya gaba a ce shi kadai za a rika ci ba.

 

Ni kuma idan na ci abinci mai maiko kamar kifi ko nama ko kwai jikina ba ya mini dadi. Ko me ya sa? Ina neman shawara.

Daga Nazifi A. 

 

Amsa: To ka daina hada su da mai na girki mana, kamar na suya. Wato sai ka rika dafawa, ko a maka farfesu, maimakon suya, don hakan zai rage maka maikon. Watakila man da kake amfani da shi ne ke sa maka ka rika jin wani iri.

 

An ce wai zukar hayakin sigari yakan kawo bakin tafin hannaye da na kafafu. Shi ne na ke tambayar ko wannan bakin yana da magani?

Daga Abdussalam, Gusau

 

Amsa: E, taba sigari za ta iya samar da sinadarai na guba da za su iya taruwa a karkashin fata. Masana sun tabbatar da cewa barin shan taba sigari ga mai sha, zai iya dawo da lafiyar mutum ta koma yadda yake a da kafin ya fara sha, sai dai sun kara da cewa hakan fa yana daukar lokaci. Misali mai shan taba sigari yana cikin hadarin kamuwa da ciwon daji na huhu da na mafitsara, amma idan ya daina sha gaba-daya, sai an dan samu shekaru kafin wannan hadarin ya ragu. Kenan idan ka daina zuka a yau, sai bayan wasu ‘yan watanni ne ko ma shekara, za ka iya neman wannan baki na tafin hannaye da kafafuwa ka rasa, ba bayan kwanaki ba.

 

Ko bacin rai na iya tayar da ciwon asma? Domin ni nakan samu haka, kuma ko na sha magani ba na dawowa daidai.

Daga Aisha U.H

 

Amsa: E, bacin rai da shiga kunci zai iya tayar da ciwon asma, wanda watakila ma ba magungunan da kike sha ne za su kwantar da ita ba, watakila sai an ba ki magungunan ta wata kafa, kamar ta kafar inhaler ko injin nebuliser. Kamata dai ya yi duk lokacin da tarin mai asma ya tashi ya yi tsanani, ya sha maganinsa ya ji bai ji sauki ba, to a garzaya da shi dakin kar-ta-kwana na asibiti mafi kusa, domin tashin tarin asma na daga cikin abubuwan da kan sa a ziyarci dakin kar-ta-kwana na emergency.

 

Da gaske ne kallon koriyar kala kamar korayen itatuwa da furanni da koren fenti na kara lafiyar idanu?

Daga Nasiru Kainuwa

 

Amsa: A’a a kimiyyance bamu san wannan ba, babu wata kala da ta fi wata a bangaren abin da ya shafi lafiyar idanu.

 

Ni idan na sha shayi da madara bayan wani dan lokaci idan na yi fitsari nakan ji kamshin madara a fitsari na. Ko hakan matsala ne?

Daga Bala Abu, Sokoto

 

Amsa: A’a ba wata matsala ba ce in dai kai a karan kanka lafiyarka kalau, kuma ba kalar madarar ka gani kuru-kuru a fitsarin ba. A wasu lokuta idan mutum ya sha shayi ko shayin kofi da madara zai iya jin kamshin shayin ko kofi ko madara a fitsarinsa, dan kamshin na nufin koda ta tace abinda jiki ba ya so.   

 

Me ke kawo jini ya sauka, akasin hawan jini?

Daga Bello Tata, Kano

 

Amsa: Duk abin da zai sa jini ko ruwa ya fita daga jiki kamar zubar jini da amai da gudawa, zai saukar da karfin bugun jini. Sai kuma shan magunguna na hawan jini, wanda aikinsu kenan su saukar da jini. Wasu magunguna wadanda ba na hawan jini ba ma za su iya sa karfin bugun jini ya sauka. Akwai ma zazzabi da ciwon zuciya, duka za su iya kawo wannan matsala.