✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mene ne bambancin ’yan siyasa da ’yan ta’adda?

Suna yin wannan ne, ba domin maslahar al’umma ba, a’a, suna yi ne kawai don maslahar kawunansu.

Wallahi, wallahi, wallahi ni dai ban ga wani bambanci ba a tsakanin dan siyasa, ko ma’aikacin gwamnatin da zai sace dukiyar al’umma, ya jefa su a cikin halin ni-’ya-su da ’yan kungiyoyin ta’addar Boko Haram da ISWAP da Ansaru da barayin daji (kidnappers/bandits) da sauransu.

Ba su da wani bambanci sam.

Kai har ma gara wadancan ’yan ta’adda da duk wani azzalumin da yake zama sanadiyyar jefa al’ummarsa cikin tashin hankali da ayyukansa munana, ayukkan kazanta, ayukkan halin beraye da gafiya!

Ya tara dimbin dukiya, wadda ta fi karfin amfaninsa ko bukatarsa, kawai don ya ji dadi shi da iyalansa da ’ya’yansa, alhali al’ummarsa suna ta tagayyara!

Ku sani, ya ku ’yan uwana masu girma! Wadancan ’yan ta’adda fa kawai za su cutar da wanda kaddara ta fada a kansa ne da ayyukansu. Su kuwa masu sace dukiyar al’umma gaba daya al’ummar suke halakawa.

Sannan kuma ku sani, duk wadancan kungiyoyin ta’addanci da muke da su, suna addabar al’umma, wallahi sun samu ne sanadiyyar ayukkan wancan barawon dan siyasa, da wancan barawon ma’aikacin gwamnati da masu taimaka masu domin su aiwatar da wannan mummunar barna, wadanda kuwa ana iya samunsu a cikin kowane jinsin mutane.

Akwai masu taimaka musu a cikin ’yan kasuwa, akwai su a cikin ma’aikata, akwai su a cikin jami’ai daban-daban, kai ina mai yi maku rantsuwa da Allah, har cikin malaman addini, na Musulunci da na Kirista, akwai masu taimaka wa gurbatattun can, domin a saci dukiyar al’umma, a durkusar da al’umma a dan sam masu wani abu!

Kai har ma ga su nan a cikin kungiyoyin da aka kafa da sunan taimakon addini, amma cutar da addinin suke yi. Sun hallaka al’umma, sun rikitar da al’umma, sun jefa rudani da tashin hankali a cikin al’umma, amma abin takaici, har yanzu ba mu gane hakan ba.

Yanzu haka jinin wasu ’yan uwanmu daga cikin wannan al’umma yana nan yana ci gaba da kwarara; an saci wasu an shiga da su daji, an kashe wasu, an kone motoci da dukiyoyin wasu, an hana jama’a da dama zama a garuruwansu, ana yi wa matanmu da ’ya’yanmu fyade, an tayar da dubban kauyukanmu sun zama kangaye, sun zama kufai, an talauta al’ummarmu da sunan biyan kudin fansa, an hana miliyoyin mutanenmu yin aikin gona, a jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja da sauran jihohin Arewa.

Amma duk da haka, abin kunya, abin mamaki, abin takaici, abin ban-haushi, wallahi, yanzu haka da nake wannan magana, wasu miyagu daga cikin wannan al’umma suna can sun tare a garin Abuja, suna yi wa ’yan siyasa kamfe.

Kuma ku ji fa, duk suna yin wannan ne, ba domin maslahar al’umma ba, a’a, suna yi ne kawai don maslahar kawunansu.

Allah wadaran naka ya lalace! Ba komai, ku ci gaba da yi, muna kallon ku, al’umma tana kallon ku, kuma wallahi talakawa suna sane da duk wani danyen aiki da kuke aikatawa. Ba addini ne a gabansu ba, ba kuma Arewa ce a gabansu ba, ba kuma al’ummarsu ce a gabansu ba.

Sun sayar da mutuncinsu da ’yan kudi kadan, kuma suna neman su sayar da addinin Allah da al’ummar Annabi Muhammad (SAW), da ’yan kudi kadan. Wallahi karyarku ta sha karya! Kifi na ganin ka mai jar koma!

Daga Imam Murtadha Muhammad Gusau. 08038289761