✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mene ne amfanin rogo da dankali a jikin dan Adam?

Mene ne amfanin rogo da dankali a jikin mutum? Ko akwai wata illa idan mutum ya fiya cin su? Amsa: Rogo da dankali su ma…

Mene ne amfanin rogo da dankali a jikin mutum? Ko akwai wata illa idan mutum ya fiya cin su?

Amsa: Rogo da dankali su ma nau’i ne na abinci da ke rukunin abinci mai ba  da kuzari kawai. Sai dai dankali shi yana da sauran rukunin abinci ‘yan kadan kamar na protein da ma’adinai da bitaman. Dankalinmu na Hausa ma ya kamata kuma ka san ya fi na Turawa wadannan sinadarai.

Rogo ne idan aka fiye cinsa zai iya sa illa kamar ta kumburin ciki saboda sinadaransa masu kawo iska ko gas a ciki, ga kuma gubar cyanide ‘yar kadan da ke cikinsa. Amma idan jefi-jefi ake ci da wuya sinadarin ya taru har ya yi illa.

 

Na dade ina shan kofin shayi a kowace safiya. To sai na lura kofin da nake amfani da shi ya yi duhu sosai. To ko wannan shayin da ya sa kofi duhu zai sa hanjina ma duhu?

Daga Fadimatu A. Birnin Kebbi

Amsa: A’a ai shi hanji abu ne mai rai, ba kamar kofi maras rai ba, da sai kin wanke. Kofin ma akwai abinda za ki sa masa duk duhun ya fita. Shi ma hanji haka yake wanke kansa da kansa ta hanyar amfani da sinadarai masu karfi ga abinda aka ci, amma marasa illa ga shi kansa hanjin. Misalan ruwan da hanji kan fitar don tsabtace kansa sune na acid da na ruwan madaciya da shi kansa ruwan hanji, don tace abinci da wankin cikin gaba daya.

Ni na kasance ina cin taliyar indomi kullum sau uku a rana. To sai na ji ana cewa za ta iya mini illa. Kuma ni na ga ba na kiba.

Daga Sarkin Indomi

Amsa: E, kuma a’a. Tabbas kana cin abinci, amma ka ga ita wannan taliya ba abinci ba ce da za a ce tana da balanced diet, wato abinci mai kunshe da abubuwan amfani duka da jiki ke bukata a kowace rana. Indomi ajin abinci mai ba da kuzari ne kadai, ba ta da abubuwa mai gina jiki, ba sinadaran ma’adinai, sai dai idan kana hadata da kwai ko kifi ko nama ko awara, da ganyaye a gefe kamar su latas da karas. To idan kana mata irin wannan hadi za ta iya zama abinci.

Ni ma ina yawan cin indomi da kwai safe da dare kafin na kwanta. Amma mutane sun ce haka na iya sa kiba.

Daga Alhaji G.B.S., Kano

Amsa:  E, ai ka san duk abu da aka ce ya yi yawa ba lafiya ba ne. Ba taliyar indomi ba, ko shinkafa kake ci haka safe da rana da dare a kullum ai dole in dai ba ka motsa jikin zazzage shi za ka yi kiba. Kuma kai ma kamar ba ka karawa da kayan abinci da za su rage maka sha’awar abinci kala daya, irinsu ganyaye da kayan itatuwa. 

Ko cin fara yana da amfani ga lafiya ko akasin haka? Domin na ga wasu suna soya ta da man ja suna ci.

Daga Manniru Abbatuwa, Kano

Amsa: E, ai ka san an ce Allah daya gari-bamban. Cin fari ba wani abu ba ne ga wadanda suka saba. Idan ka lura wata al’umma ce daban suka fi ci kamar ‘yan kudu da ‘yan kasar Sin wato China. Kai ma kuma akwai abincinka da sukan gani su ga ba za su iya ci ba. Tabbas a kimiyance fari na da sinadarai masu gina jiki na protein, kamar irin wanda ake samu a kananan kifin nan na crayfish. Ka ga ma ai kusan girmansu daya, amma kai watakila za ka iya cin wannan kifi ba ka ci fari ba.

 

Na yi tambaya amma ba a fahimta ba. Ina yawan tashi fitsari ne ba yawan fitsarin kwance ba kamar yadda aka buga.

Daga Isma’il, Lagos

Amsa: E, kwarai ba a fahimci Hausar taka ba. Ka ga da ka rubuto fitsarin kwance ai likitan mafitsara aka ce ka gani, amma yanzu da ka gyara, sai a ce maka likitan jiki gaba daya wato internal medicine za ka gani. Da fatan za a gyara rubutu, kamar yadda masu zaven gidan rediyo kan ce.

 

Ni kuma idan na yi fitsari da safe ba na sake yi sai da dare. Ko hakan akwai matsala?

Daga Muhammad Auwal, Zaria

Amsa: Ba wata matsala, sai dai kawai yana nuna watakila ba ka shan ruwa sosai.

 

Daga shekaru nawa ne idan mutum hakorinsa suka fadi ba za su sake fitowa ba? Domin ni na fadi a shekarun baya hakorina ya valle sai na ga wani kamar yana fitowa a yanzu. Kuma ga shi na kai shekaru 30

Daga Ahmed, Maiduguri

 

Amsa: Ai daga shekarun bayan famfara, wato daga shekaru 6-9 bayan hakora sun cika, idan hakorinka ya sake faduwa to sai dai ciko Mallam Ahmed. Wancan da ka gani sai dai ko ragowar wanda ya fadi ne. Sai dai kuma daga shekaru ashirin sama, akwai wasu turamen can karshen baki daga baya nan ma za su iya fitowa, za su iya kasancewa sune ka jiwo.

 

Me ke kawo hakori ya yi zafi kau, kai ya rika nauyi idan an sha ruwan sanyi ko na zafi?

Daga Suraj dan Murja da Kabiru Tashar Jabi

Amsa: Ga alama hakorin gefen wurin da aka ji ya amsa idan aka sha ruwan sanyi ko na zafi, yana da matsala. Yawanci dai ba ya wuce cinyewa da kwayoyin cuta suke masa, ta yadda idan aka sha abu mai sanyi ko mai zafi yakan tavo jijiyar laka ta karkashin shi hauren maras lafiyar, har ma gefen fuska da kai su amsa. Da fatan za a daure a je likitan hakori ya gani ko haka din ne.

 

Ko irin mayukan nan na yaji masu madaukin menthol da ake shafawa a hanci suna da illa?

Daga Ahmed, Bichi

Amsa: A’a mayukan mura na hanci masu yajin menthol da sauran ire-irensu ba su da illa, saboda iyakar aikinsu kenan a nan, su samu su dan sumar da kwayoyin virus don murar ta yi sauki.