✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa ruwan famfo ke da tsada a Kano?

Ruwa shi ne ginshikin rayuwa kuma sinadarin hada duk wani abu na rayuwa kama daga abinci, ibada da sauran al’amura.Ruwa na da muhimmiyyar rawa wajen…

Ruwa shi ne ginshikin rayuwa kuma sinadarin hada duk wani abu na rayuwa kama daga abinci, ibada da sauran al’amura.
Ruwa na da muhimmiyyar rawa wajen taimakawa don gudanar da ayyukan rayuwa, kamar yadda na yi bayani, Ana amfani da ruwa wajen gudanar da ibada irin su alwala da wanka da sha da wanki da dafa abinci da wanke-wanke da makamantansu.
Ruwa ya ka su kashi da dama, kama daga ruwan famfo, wanda al’umma kan biya a karshen kowane wata; sai ruwan rijiya, wanda mutane kan gina, su tono don biyan bukatunsu, ya alla ba su da ikon biyan kudin ruwa na wata-wata, ko unguwar da suke ba a samun ruwan famfo, sai kuma ruwan burtsatse, wanda masu hali ko hannu da shuni kan gina don gudun hantara ko wulakanci daga ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha, wasu kuma na ginawa ne don su bai wa al’umma ko kuma rukunin gidajensu ba a samun ruwa, kuma suna da yawan bukatarsa.
A yayin da jihohi kamar Katsina ke biyan Naira 500 zuwa Naira 900 a matsayin kudin ruwa a karshen kowane wata, Jihar Gombe na biyan Naira 200, Jihar Bauchi na biyan Naira 500, Jihar Kaduna na biyan Naira 840 zuwa Naira 2,000, Jihar Jigawa na biyan Naira 200, tare da samun ruwa na a kalla sa’o’i 15 zuwa 20 cikin awa 24, sai ga shi abin mamaki da takaici a Jihar Kano al’umma na biyan Naira 1,500 zuwa Naira 2,300, alhalin kuma ba a samun ruwa na awa 10 a rana. Ruwa ya dade yana zuwa shi ne awa biyar, wani lokaci ma sai a yi kwana biyu ba ruwan, amma karshen wata na zuwa sai hukumar ta duba in gidanka da kyau ta rubuta maka Naira 2,300, idan kuma aka ga gidan ba wani ba ne sai a rubuta maka Naira 1,500. In takaice muku a Jihar Kano ba inda ake kai bill na ruwa kasa da Naira 1,500 sannan ruwan ba ya samuwa yadda ya kamata. Koda ana samun ruwan awa 24 bai kamata a ce kudin sun kai haka ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda harkokin tattali da kasuwanci suka tabarbare.
Tambayar a nan ita ce, me ya sa Hukumar Ruwa ta Jihar Kano ke karbar wannan kudi masu yawa a hannun al’ummarta, ba tare da lura da yanayin da ake ciki ba? A shekarun baya daga 2011 ana biyan Naira 600 a matsayin kudin ruwa daga baya ya koma Naira 1,000 ana nan ya koma Naira 1,500 aka wayigari yanzu ya koma Naira 2,300 ba mu san me gobe za ta yi ba mai yiwuwa su cike ya koma Naira 3,000.
Da ka tambayi ma’aikatan hukumar dalilin karin kudin, ko me ya sa a Jihar Kano ake biyan kudin ruwa da tsada, sai su ce wai saboda sayen sinadarai (Chemicals) da ake zubawa ne wajen tace ruwan kafin a turo shi. Amma ni ina ganin wannan ba dalili ba ne, ko sauran jihohin ba sa sayen chemicals din don yin amfani da shi ne?
Ina roko ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan Ruwa da Shugaban Hukumar Samar da Ruwan su dubi wannan koke na al’ummar Kano da idon basira da rahama, domin kuwa ba kowa ne zai iya biyan wannan kudin ba. Sannan hakan na ba da dama ga wasu ma’aikatan hukumar su rika amsar wani abu a maimakon kudin ruwan a wajen masu gidaje, don ci gaba da amfani da ruwan. Ka ga a nan ba a yi wa masu biya adalci ba.
-dangida, dan jarida ne da ke zaune a Lamba 13, Zoo Road, Jihar Kano. 08033195532