✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke kawo qaruwar luwaxi da maxigo a Najeriya?

A yau JAMILU SANI RARAH SAKKWATO (07031960698), ya yi tsokaci ne game da munanan xabi’un nan na luwaxi da maxigo da ke wakana cikin al’ummar…

A yau JAMILU SANI RARAH SAKKWATO (07031960698), ya yi tsokaci ne game da munanan xabi’un nan na luwaxi da maxigo da ke wakana cikin al’ummar qasar nan. Ga abin da yake cewa:

Idan aka ce luwadi ko madigo (namiji ya sadu da namiji/mace ta sadu da mace), hakika babu wani addini guda a duniyar nan da ba ya kyamarsa. Amma babban abin takaici shi ne, wannan muguwar dabi’a ta yawaita a Najeriya. Babban abin bakin ciki da ban haushi shi ne, har da Arewarmu, wannan dabi’ar ta yawaita.

Na yi ta samun labarai game da wannan muguwar dabi’ar ta neman maza. Daga cikinsu akwai labarin da ya tayar mini da hankali ainun tare da jefa ni cikin tunani. Wadansu matasa ne biyu, dan shekara 31 da dan shekara 25 suka kulla wata (haramtacciyar) yarjejeniya game da luwadi.

Yarjejeniyar ita ce, dan shekara 31 yana da sabon babur, shi kuma dan shekara 25 yana son irin wannan babur din. Shi ne suka kulla yarjejeniyar zai yi lalata da shi sau 100, ma’ana za su yi luwadi har sau 100 (wa’iyazubillah) sannan ya ba shi wannan babur.

A kullum mai babur din ya bukace shi (domin yin luwadi), sai ya kira shi ya je su yi wannan fasadin. Sai da ya yi lalata  da shi har sau 75 sannan dan luwadin ya ce, shi a gaskiya ya gaji da kwanciya da shi (saboda yanzu ba ya jin dadinsa). To, a haka suka rika rigima har asirinsu ya tonu, aka je kotu domin shari’a.

Ana haka sai wani abokina ya kira ni domin mu je amsar wani bakonsa da ya yi dare, ’yan sanda sun kama shi. Mun je kawai sai ga motar ’yan sanda ta dawo dauke da wadansu da suka sake kamowa su biyu. Wadannan mutane, dukkansu zigidir suke haihuwar uwarsu. An kamo su ne a bayan wani kango suna luwadi!

Kasancewa ban taba ido biyu da irin wannan rikici ba, hankalina ya yi matukar tashi. Bayan an zaunar da su, ana tambayarsu me ya sa suke wannan lalata a tsakaninsu? Shi ne dayan ke cewa wai wandon jins biyu ya yi alkawarin zai saya masa.

Babu shakka Yahudawa sun yi gaskiya da suka ce: “Idan kuna son ku karya kasashen Musulmi, to ku karya tattalin arzikinsu.” Babu shakka talauci da rashin hakuri su ne manyan musabbaban wannan muguwar dabi’a a cikin al’umma. Don haka ina son in ba matasa shawara, a rayuwa yana da kyau su rika duba gaba, domin muddin aka lalata maka rayuwa, zuwa gaba za ka yi nadama wacce ba ta da amfani. Su san cewa babu shakka duk wanda ya yi wannan lalatar da kai, to shi bukatarsa ta biya kuma ba ka sake ba shi sha’awa kamar yadda labarin mai babur ya nuna.

Kamar yadda na fada cewa, talauci na daga cikin manyan sabubban da suke kawo neman maza, musamman a Arewa, idan muka koma tarihi, za mu fahimci gaskiyar haka.

Sa Frederick Lugard dan kasar Ingala, a ranar 1 ga Janairu, 1914 ya yi amfani da alkalami da hikimarsa, ya hada Arewa da Kudu suka zama kasa daya, Najeriya. To, tun daga wancan lokaci aka dauki niyyar yakar Arewa a boye, kasancewa an san talauci mugun abu ne.

Bayan Najeriya ta zama kasa daya sai aka yi kokarin koya wa mutanen Kudu neman kudi da yadda za su rika tallafa wa ’yan uwansu, domin su zamo masu taimakon junansu. A yau, idan ka dubi ’yan Arewa, za ka tarar cewa mafi yawanmu ba mu damu da taimaka wa junanmu ba. Ina ganin wannan shi ya sanya talauci ya fi kamari a Arewarmu tare da rashin son taimaka wa juna.

Yanzu wani abin ban haushi da bakin ciki shi ne, kwanan baya na samu labarin cewa an kama wani bawan Allah yana luwadi da yara biyu, wadanda kowane daga cikinsu ya kai shekara 22. Bayan an kama su ake tambayarsu abin da ya ba su har yake lalata da su, shi ne suke cewa, Naira dari biyu yake ba kowannensu duk lokacin da zai yi wannan lalata da su!

Sannan wani ya taba gaya mini cewa da idonsa ya ga wadansu suna lalata a tsakaninsu. Ya tarar da mutum uku, daya yana saman mace, daya kuma ya zo yana yi masa luwadi.

Shin ’yan Arewa, yaushe za mu tashi mu yaki wannan matsala ce? Yaushe hankalinmu zai dawo gare mu ne? Na san wani zai ce bai san yadda zai taimaka a yaki wannan matsala ba, to idan har ba ka sani ba, ga wasu hanyoyi da na zakulo domin yakar wannan mummunar dabi’a.

1-Da farko idan kun kama mai yin wannan muguwar dabi’a a unguwarku, ku yi sauri ku garzaya da shi ga hukuma domin a hukunta shi. Domin barinsu a cikin al’umma yana daga cikin musabbabin yawaitarsu.

2-Idan ka ga wani dan uwanka, kanenka ko abokinka yana abota da wanda ke wannan lalatar, to yi maza ka sanar da shi halinsa. Domin takan yiwu yana zaune da shi ne, bai san halinsa ba. Amma idan ka sanar da shi, ka ga ba su rabu ba, to shi ma ka yi hankali da shi.

3-Idan ka ga dan uwanka cikin matsalar kudi ko yana neman wani taimako, kira shi ka taimake shi, kuma ka yi masa wa’azi a kan dogara da Allah. Ma’ana, ka sanar da shi cewa, duk abin da ya ga ya samu daga Allah ne; haka idan ma ya rasa daga Allah ne, don haka kada zuciyarsa ta jefa shi cikin tunanin banza.

4-Ka rika sanar da abokanka da kannenka labarin irin ukubar da aka yi wa mutanen Annabi Ludu (AS) da kuma binciken da likitoci suka yi a kan masu yin wannan lalata.

Babu shakka wadannan abubuwa za su taimaka sosai wajen yakar wannan matsala. Na san da yawa akwai wadanda tuni sun fada cikin wannan muguwar dabi’a ta neman maza, to idan har suna so su daina, ga wasu shawarwari:

Ku sani cewa zunubi kamar ciwo ne, mataki-mataki ne. Akwai wanda ke bukatar ’yan kwayoyin magani kadan sai ya ba da baya. Akwai mai bukatar kulawar likitoci da shawarwari da nacewa ga shan magani. Wani ciwon sai an yi tiyata, an fede, an cire shi.

To, zunubin luwadi ko madigo na bukatar kulawar likitoci da shawarwari da nacewa ga shan magani. Da farko, dole ka yi tuba ta gaskiya. Na san wani zai ce ai Allah ba zai yafe masa ba. Wa ya gaya maka Allah ba zai yafe ba? Hakika, Allah babu abin da ba Ya yafewa, matukar bawa ya yi tuba ta gaskiya; tubar da ake kira tuba.

Bayan tuba kuma akwai bukatar ka kaurace wa abokan da kake wannan lalata da su. Kuma ka samu malamai na Sunnah su rika gabatar maka da shawarwari tare da ba ka labarin irin ukubar da Allah (SWT) Ya shirya wa masu wannan lalata.

Wani abin burgewa ya faru a nan Arewa. Wani matashi ne Allah Ya jarrabe shi da fadawa cikin wannan masifa ta neman maza, har ta kai ba ya sha’awar mata sai maza. Daga lokacin da ya ji tarihin halakarwar da Allah Ya yi wa mutanen Annabi Ludu (AS) da kuma azabar da Allah (SWT) Ya tanadar wa masu wannan lalata, nan take sai ya tsorata, ya tuba. Bayan ya tuba kuma sai ya mayar da masallaci wurin zamansa da wurin hirarsa; kullum shi ne istigfari tare da neman shawarwarin malamai.

Ai kuwa cikin taimakon Allah, nan take sha’awarsa ta mata ta dawo kuma alhamdu lillahi har ya yi aure, ya haifi ’ya’ya, kuma yanzu haka shi ne ladanin unguwarsu.

Don haka ’yan uwa da suka samu kansu a cikin wannan matsala, su daure su tuba, ko Allah zai jikansu. In kunne ya ji, hakika jiki bai tsira, sai ya yi aiki da abin da ya ji. Allah Ka shiryar da mu hanyarKa madaidaiciya, amin.