✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke jawo kwarewa, sannan ya ya za a kiyaye faruwarta?

Amsa: kwarewa na faruwa ne idan wani abu da aka sa a baki walau abinci ko ruwa, ko ma wani abu da ba ci ake…

Amsa: kwarewa na faruwa ne idan wani abu da aka sa a baki walau abinci ko ruwa, ko ma wani abu da ba ci ake ba (kamar hadiyar kwandala a yara) ya bi hanyar numfashi maimakon hanyar abinci.

Da yake ka tambaya hanyoyi ko kofofi nawa ne a makoshin dan Adam, za a iya ce maka guda hudu ne, akwai hanyar da ta fado daga sama, hanyar hanci kenan, akwai wadda ta bude zuwa huhu, wannan hanyar iska kenan, akwai kuma wadda ta bude zuwa tumbin ciki, wadda ita ta abinci kenan. Akwai kuma wasu ‘yan kanana a kowane gefen makoshi da suka bude a sashin dama da na hagu, wadanda suka tafi cikin kunne. Iska na shigowa ko dai ta hanci ko ta baki, ko ta duka biyun, sai ta wuce huhu ta hanyar numfashi wadda ke bayan hanyar abinci. Iska za ta iya shiga hanyar abinci ba a samu matsalar komai ba da zai wuce gyatsa, amma abinci ba zai iya shiga hanyar iska ba mutum ya zauna lafiya. Wannan ita ce kwarewa.

Da zarar abinci ko abin sha ya taba hanyar iska kofofin ke kokarin rufewa da hankado ko ma mene ne ta hanyar tari mai karfi. To wannan tarin shine idan aka ci sa’a sai abinda ya so shiga huhun ya dawo ko dai a fitar da shi ta baki ko kuma a hadiye shi cikin tumbi, ya bi hanyar abinci ke nan. Amma idan aka yi rashin sa’a abin da zai wuce hanyar numfashin ya riga ya wuce ko ya tokare hanyar numfashi ba a samu damar tari ba, to abin zai iya sa numfashin mutum ya tsaya cak, ta yadda idan ba a ciroshi cikin gaggawa ba zai iya halaka mutum cikin kankanin lokaci. Kamar yadda aka ba da labarin wani mutum a kasar Ingila makonni biyu da suka shige da yake takamar zai iya hadiye wani dan kifi da ranshi. Ai ko da ya daga kai ya bude baki ya saki kifin nan, sai kifi ya yi tsalle wuf ya koma hanyar iska zai shiga, wato bai shiga hanyar ciki ba, inda da nan ya dosa da za a hadiye shi. Nan da nan kuwa mutuminka ya rike wuya ya kasa numfashi saboda kifi ya toshe hanyar iska, kafin ka ce kwabo mutum ya fadi ya suma saboda tsayawar numfashi. Amma da yake da sauran kwanansa a gaba, nan da nan aka kira masa masu agajin gaggawa na kar-ta-kwana. Cikin mintoci kadan suka iso suka ji abin da ya faru, dayansu ya fito da kayan aiki ya haska makoshin ya gano jelar kifin ya sa mariki ya jawo shi da kyar. Nan da nan numfashi ya dawo.

To ban da irin wannan kasada abubuwan da kan jawo mutum ya kware sun hada da yawan surutu ko dariya ko tafiya ko gudu yayin cin abinci. Wasu kuma sukan kware ne yayin da suka sa katuwar loma a baki, saboda lomar ta yi wa hanyar abinci girma, sai wata ta gutsure ta tafi hanyar iska. Wannan a manya kenan, mun taba bayanin abubuwan da kan kawo hakan a yara.

To yadda za a kiyaye matsalar kenan ba ta wuce a daina kasadar saka abubuwa a baki ba domin wasa, sai kuma daina surutu da dariya yayin cin abinci. Sai kuma nutsuwa da zama wuri daya yayin cin abinci. Tunda babbar loma ma na iya shake mutum, dole ke nan mutum ya san irin lomar da zai yi wadda ba za ta cuce shi ba.

Daga karshe kuma idan aka ga wani ya kware har ya kasa numfashi sai a yi maza a kira masa ‘yan agajin lafiya na kar-ta-kwana idan akwai su a garin, ko a shirya yadda za a kai shi asibiti. Kafin su zo kuma sai a yi kokarin fitar da abin da ya shake mutumin. To ya ake kokarin fitar da abin? Ba hannu za a sa a bakin mutum a yi ta lalube ba, a’a zuwa ake bayan mutumin a tasar da shi tsaye a zuro hannaye kan tumbin cikinsa a yi ta dannowa sama har sai abin da ya shakes hi ya fito, kamar yadda za a gani a hoton sama.

Me ke sa wasu mutane barcin zomo? Wato suna barci amma idanunsu a bude? Hakan larura ce ko kuwa?

Daga Haruna Muhammad, Katsina

Amsa: To wannan ma a kimiyyance idan kullum mutum ke samun matsalar, to daga gira ne. Masana kimiyyar barci suna ganin matsalar murfin ido ce kan sa mutum ya rika barci haka, don haka watakila idan matsalar ta dade watakila ma har tana sa bushewar ido sai an dangana da likitan ido.

Ko ya dace a sha ruwan rijiyar burtsatse wadda ke jikin katangar makabarta? Domin muna da rijiya da ke jikin makabarta da muke shan ruwanta

Daga Shehu Ali, Katsina

Amsa: A’a bai dace a sha ruwan rijiyar da aka gina a jikin bangon makabarta ba. Su wadanda suka gina rijiyar watakila sun yi ne don dalilin aikin hakar kabari da sauran aikace-aikacen makabarta. Amma a kimiyyance ruwanta bai kamata a sha ba tunda a jikin katangar makabartar take. Da a ce akwai tazarar taku da yawa kamar kafa 50 tsakanin makabartar zuwa rijiyar to da da sauki, kamar idan a tsallaken titin makabartar take.

Ni ko idan na ci abinci bayan wasu mintuna sai ya dawo bakina. Shine nake tambaya hakan ko ciwo ne.

Daga Muhammad Kumo

Amsa: E, akwai irin wannan matsala a wasu kalilan din mutane a cikin al’uma, wanda a likitance ya fi kama da abinda muke kira rumination syndrome wato ciwon cin abincin dabbobi. Matsala ce babba da dole sai ka je asibiti bangaren ciki ka musu bayani, sa’annan za su ga yadda za su bullowa lamarin.

  

Mene ne ke sa mutum ke fitsarin jini akai-akai?

Daga Abbas, Tafawa balewa

Amsa: Cutuka irinsu shigar kwayoyin cuta iri-iri kamar na tsargiya da sauransu. Sai kuma tsuro ko kari a tantanin fitsari, sai kuma tsakuwa a mafitsarar kamar a koda ko a ita kanta tantanin tara fitsari da ke mara. Duka wadannan za su iya jawo fitsarin jini. Amma mai wannan matsala ba zama zai yi ya zura wa sarautar Allah ido ba, a’a asibiti zai je a aunashi a gano dalilin, wato daya daga cikin wadancan abubuwa da aka lissafa, idan an gano kuma a ba shi magani.