✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD Za Ta Samar Da Sabon Tsarin Zaman Lafiya A Kaduna Da Katsina

Majalisar Dinkin Duniya, za ta samar da wani tsari mai suna "Karfafa Zaman Lafiya a Kananan Hukumomi da Jihohin Katsina da Kaduna

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya dauki nauyin samar da wani tsari mai suna “Karfafa Zaman Lafiya a Kananan Hukumomi da Jihohin Katsina da Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya”.

Yankin Arewa maso Yamma, musamman jihohin Kaduna da Katsina, na fama da matsalolin da suka shafi rikicin manoma da makiya, da rikicin kabilanci da ta’addanci da sauransu.

Domin samun nasarar tsarin, an gudanar da wani taro na musamman a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, don neman goyon baya da tabbatar da zaman lafiya da yaki da ’yan bindiga musamman a jihohin Kaduna da Katsina.

Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Matthias Schmale, ya ce, babban dalilin kafa Majalisar Dinkin Duniya shi ne samar da zaman lafiya tsakanin kasashe. Don haka, ya zama wajibi majalisar ta tabbatar an samu zaman lafiya a duniya tare da kai ɗauki ga musamman jihohin Katsina da Kaduna bisa yadda suke buƙatar taimako.

A nashi ɓangaren, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya bayyana cewa: “A halin yanzu kananan hukumomi 8 da ke maƙwabtaka da Nijar na fuskantar hare-haren ’yan bindiga. Bugu da kari, akwai kananan hukumomi sama da 14 baya ga wadannan 8, da a kowace rana ina samun rahotanni kan hare-haren da ake kai wa kauyuka a cikinsu.”

Gwamnan ya kara da cewa: “An dauki jami’an tsaro tare da tura su kauyukan domin dakile hare-haren da ake kaiwa a yankunan”.

Har ila yau, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani wanda mai ba shi shawara na musamman kan samar da zaman lafiya, Atiku Sanke, ya wakilta, ya ba da tabbacin goyon baya wajen ganin an samar da ayyukan da za su tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Babbar manufar shirin mai lakabin PBF I4P, ita ce karfafa wa gwamnatocin jihohin kwarin gwiwa don samar da hadin kai da hanyoyin zaman lafiya da rigakafin matsalolin da rikice-rikice suke haifarwa.

Hukumomin da suka hadu wurin samar da wannan sabon tsari na zaman lafiya sun hada da: UNDP, Sashen Kula da Mata na MDD (UN Women), da IOM tare da tallafin Cibiyar OHCHR, domin bayar da gudunmawa ga mutunta hakkin Da’adam.